Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Resurrection

194 ayoyi · 3 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. In ba a tashe Kiristi ba kuwa, ai, wa’azinmu, da bangaskiyarku banza ne.

  2. Sai ma ya zama mun zama masu ba da shaidar ƙarya game da Allah ke nan, domin mun shaida game da Allah cewa ya tashe Kiristi daga matattu. Bai tashe Kiristi ba ke nan, in lalle ba a tā da matattu.

  3. Gama in ba a tā da matattu ba, to, Kiristi ma ba a tashe shi ba ke nan.

  4. In kuwa ba a tashe Kiristi ba, bangaskiyarku a banza take, ya zama har yanzu kuna cikin zunubanku ke nan.

  5. Ashe, waɗanda suka yi barci a cikin Kiristi ma sun hallaka ke nan.

  6. In a wannan rayuwar ce kaɗai muke da bege cikin Kiristi, mun zama abin tausayi fiye da dukan mutane.

  7. Amma tabbatacce, an tā da Kiristi daga matattu, nunan fari kuwa cikin waɗanda suka yi barci.

  8. Da yake mutuwa ta zo ta wurin mutum, haka tashin matattu ma ya zo ta wurin mutum.

  9. Kamar yadda duka suka mutu cikin Adamu, haka duka za su rayu cikin Kiristi.

  10. Sai dai kowa da lokacinsa. Kiristi ne nunan fari; sa’an nan sa’ad da ya dawo; za a tā da waɗanda suke nasa.

  11. Sa’an nan sai ƙarshen ta zo, sa’ad da zai miƙa wa Allah Uba mulki, bayan ya hallaka dukan sarauta, mulki da iko.

  12. Gama dole yă yi mulki har sai ya sa dukan abokan gābansa a ƙarƙashin ƙafafunsa.

  13. Abokin gāba na ƙarshen da za a hallaka kuwa, shi ne mutuwa.

  14. Gama ya “sa kome a ƙarƙashin ƙafafunsa.” To, da aka ce an sa “kome” a ƙarƙashinsa, a fili yake cewa ba a haɗa da Allah a ciki ba, shi wannan da ya sa kome a ƙarƙashin Kiristi.

  15. Sa’ad da ya yi haka, sa’an nan Ɗan kansa yă koma a ƙarƙashin shi wanda ya sa kome a ƙarƙashinsa, domin Allah yă zama kome da kome.

  16. To, in babu tashin matattu, mene ne waɗanda ake musu baftisma saboda matattu za su yi? In ba a tā da matattu sam, me ya sa ake yin wa mutane baftisma saboda su?

  17. Mu ma don me muke sa kanmu cikin hatsari a kowace sa’a?

  18. Ina fuskantar mutuwa kowace rana. I, kamar yadda yake tabbatacce cewa ina taƙama da ku cikin Kiristi Yesu Ubangijinmu.

  19. In na yi kokawa da mugayen namomin jeji a Afisa bisa ga ra’ayin mutane ne kawai, mece ce ribata, in har ba a tā da matattu? Ai, “Sai mu ci mu sha, da yake gobe za mu mutu.”

  20. Amma wani yana iya tambaya yă ce, “Ta yaya ake tā da matattun? Da wane irin jiki za su tashi?”

  21. Kai, marar azanci! Abin da kuka shuka ba zai tsira ba sai ya mutu.

  22. Sa’ad da kuke shuki, ba tsiron da zai yi girma ba ne kuka shuka, ƙwayar ce kawai, ko ta alkama ko kuma na wani irin dabam.

  23. Amma Allah yakan ba ƙwayar jiki yadda ya yi niyya, kuma ga kowane irin ƙwaya yakan ba ta irin jikinta.

  24. Ba dukan nama ne iri ɗaya ba. Mutane da irin nasu, dabbobi da irin nasu, tsuntsaye da irin nasu, kifaye kuma da irin nasu.

  25. Akwai jikuna iri na samaniya, akwai kuma jikuna iri na duniya; sai dai darajar jikunan samaniya dabam take, darajar jikunan duniya kuma dabam take.