Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Reptiles: Unclean and not eaten

9 ayoyi · 21 fannoni

Ayoyi game da Unclean and not eaten

  1. Dukan waɗanda suke rarrafe, za su zama marasa tsarki gare ku. Duk wanda ya taɓa su sa’ad da suka mutu, zai zama ƙazantacce har zuwa yamma.

  2. Duk wanda ya ci wani sashe na gawar dole yă wanke rigunansa, kuma zai ƙazantu har yamma. Duk wanda ya ɗauki gawar dole yă wanke rigunansa, zai kuwa ƙazantu har yamma.

  3. “ ‘Duk dabba mai rarrafe a ƙasa abin ƙyama ne; ba kuwa za a ci shi ba.

  4. Ba za ku ci wani halittar da take rarrafe a ƙasa, ko tana jan ciki, ko tana tafiya a kan ƙafafu huɗu, ko a kan ƙafafu da yawa ba; abin ƙyama ne.

  5. Kada ku ƙazantar da kanku ta wurin wani daga waɗannan halittu. Kada ku ƙazantar da kanku ta dalilinsu, ko a mai da ku haramtattu ta wurinsu.

  6. Ya ga sama ya buɗe ana kuwa saukowa wani abu ƙasa kamar babban mayafi zuwa duniya ta kusurwansa huɗu.

  7. Cikinsa kuwa akwai kowace irin dabba mai ƙafa huɗu da masu ja da ciki na duniya da kuma tsuntsayen sararin sama.

  8. Sa’an nan wata murya ta ce masa, “Bitrus, ka tashi. Ka yanka ka ci.”

  9. Bitrus ya ce, “Sam, Ubangiji! Ban taɓa cin wani abu marar tsarki ko marar tsabta ba.”