Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Reptiles

37 ayoyi · 21 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Allah kuwa ya ce, “Bari ƙasa tă ba da halittu masu rai bisa ga irinsu; dabbobi da halittu masu rarrafe, da kuma namun jeji, kowane bisa ga irinsa.” Haka kuwa ya kasance.

  2. Allah ya halicci namun jeji bisa ga irinsu, dabbobi bisa ga irinsu, da kuma dukan halittu masu rarrafe a ƙasa bisa ga irinsu. Allah kuwa ya ga yana da kyau.

  3. Sa’an nan Allah ya ce, “Bari mu yi mutum cikin siffarmu, cikin kamanninmu, bari kuma su yi mulki a bisa kifin teku, tsuntsayen sama, da kuma dabbobi, su yi mulki a bisa dukan duniya, da kuma a bisa dukan halittu, da masu rarrafe a ƙasa.”

  4. In ka ƙi barinsu, zan hore ka da annoban kwaɗi a dukan ƙasarka.

  5. “ ‘Waɗannan ƙananan dabbobi da suke rarrafe a ƙasa, haram ne a gare ku, wato, murɗiya, da ɓera, da gafiya da irinsa,

  6. da tsaka, da hawainiya, da ƙadangare, da guza, da damo.

  7. Dukan waɗanda suke rarrafe, za su zama marasa tsarki gare ku. Duk wanda ya taɓa su sa’ad da suka mutu, zai zama ƙazantacce har zuwa yamma.

  8. Duk wanda ya ci wani sashe na gawar dole yă wanke rigunansa, kuma zai ƙazantu har yamma. Duk wanda ya ɗauki gawar dole yă wanke rigunansa, zai kuwa ƙazantu har yamma.

  9. “ ‘Duk dabba mai rarrafe a ƙasa abin ƙyama ne; ba kuwa za a ci shi ba.

  10. Ba za ku ci wani halittar da take rarrafe a ƙasa, ko tana jan ciki, ko tana tafiya a kan ƙafafu huɗu, ko a kan ƙafafu da yawa ba; abin ƙyama ne.

  11. Kada ku ƙazantar da kanku ta wurin wani daga waɗannan halittu. Kada ku ƙazantar da kanku ta dalilinsu, ko a mai da ku haramtattu ta wurinsu.

  12. don kada ku lalace, ku kuma yi wa kanku gunki, siffa ta wani kama, ko a kamannin namiji, ko kuwa ta mace,

  13. ko kuwa a kamannin wata halittar da take rarrafe a ƙasa, ko na wani kifi a cikin ruwaye a ƙarƙashi.

  14. Ya bishe ku cikin hamada mai fāɗi, mai bantsoro, wannan busasshiyar ƙasa wadda ba ta da ruwa, ga macizai masu dafi da kuma kunamai. Ya ba ku ruwa daga dutsen ƙanƙara.

  15. Ruwan inabinsu dafin macizai ne, mugun dafin gamshaƙa ne.

  16. Ya yi magana a kan rayuwar itatuwa, daga al’ul na Lebanon zuwa hizzob da yake girma a bangaye. Ya kuma yi koyarwa game da dabbobi, da tsuntsaye, da abubuwa masu rarrafe, da kuma kifi.

  17. Da numfashinsa ya sa sararin sama ya yi kyau da hannunsa ya soke macijin nan mai gudu.

  18. Na zama ɗan’uwan diloli, na zama abokan mujiyoyi.

  19. Dafinsu ya yi kamar dafin maciji, kamar na gamsheƙan da ya toshe kunnuwansa,

  20. Kamar katantanwun da suke narkewa yayinda suke tafiya, kamar jinjirin da aka haifa matacce, kada su ga hasken rana.

  21. Za ka taka zaki da gamsheƙa; za ka tattake babban zaki da maciji.

  22. namun jeji da dukan dabbobin gida, ƙanana halittu da tsuntsaye masu firiya,

  23. A ƙarshe yana sara kamar maciji da kuma dafi kamar gamsheƙa.

  24. “Matsattsaku tana da ’ya’ya mata biyu. Suna kuka suna cewa, ‘Ba ni! Ba ni!’ “Akwai abubuwa uku da ba sa taɓa ƙoshi, guda huɗu ba sa taɓa cewa, ‘Ya isa!’

  25. Jariri zai yi wasa kurkusa da ramin gamsheƙa, ɗan yaro kuma zai sa hannunsa a ramin maciji mai mugun dafi.