Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Prayer Under Affliction: That we may be turned to God

5 ayoyi · 17 fannoni

Ayoyi game da That we may be turned to God

  1. Ka mai da mu, ya Allah Maɗaukaki; ka sa fuskarka ta haskaka a kanmu za mu kuwa cetu.

  2. Ka sāke mai da mu, ya Allah Mai Cetonmu, ka kau da rashin jin daɗinka daga gare mu.

  3. Za ka ci gaba da fushi da mu har abada ne? Za ka ja fushinka cikin dukan tsararraki?

  4. Ba za ka sāke raya mu ba, don mutanenka su yi farin ciki a cikinka?

  5. “Tabbatacce na ji gurnanin Efraim yana cewa, ‘Ka hore ni kamar ɗan maraƙi mai ƙin ji, na kuwa horu. Ka mayar da ni, zan kuwa dawo, domin kai ne Ubangiji Allahna.