Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Prayer Under Affliction: For pardon and deliverance from sin
Ayoyi game da For pardon and deliverance from sin
Ka cece ni daga dukan laifofina; kada ka sa in zama abin dariya ga wawaye.
Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Zabura ta Dawuda. Sa’ad da annabi Natan ya zo wurinsa bayan Dawuda ya yi zina da Batsheba. Ka yi mini jinƙai, ya Allah, bisa ga ƙaunarka marar ƙarewa; bisa ga tausayinka mai girma ka shafe laifofina.
Kada ka riƙe zunubai kakanni a kanmu; bari jinƙanka yă zo da sauri yă sadu da mu, gama mun fid da zuciya sarai.