Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Penitent

131 ayoyi · 1 fanni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Zan tashi in koma wurin mahaifina, in ce masa, “Baba, na yi wa sama, na kuma yi maka zunubi.

  2. Ni ban isa a ƙara kira na ɗanka ba. Ka mai da ni kamar ɗaya daga cikin bayinka.” ’

  3. Sai ya tashi ya kama hanya ya koma wurin mahaifinsa. “Amma tun yana nesa, mahaifinsa ya hange shi. Tausayi kuma ya kama shi, sai ya tashi ya ruga da gudu wurinsa, ya rungume shi, ya yi masa sumba.

  4. “Sai ɗan ya ce masa, ‘Baba, na yi wa sama, na kuma yi maka zunubi. Ni ban isa a ƙara kira na ɗanka ba.’

  5. “Amma mahaifin ya ce wa bayinsa, ‘Maza! Ku kawo riga mafi kyau ku sa masa. Ku sa zobe a yatsarsa, da takalma kuma a ƙafafunsa.

  6. Ku kawo ɗan saniya mai ƙiba ku yanka. Bari mu yi biki mu yi shagali.

  7. Gama ɗan nan nawa, da ya mutu, amma yanzu yana da rai kuma. Da ya ɓata, amma yanzu an same shi.’ Sai suka fara shagali.

  8. “Yayinda ake haka, babban ɗan yana gona. Da ya zo kusa da gida, sai ya ji ana kiɗi ana rawa.

  9. Sai ya kira ɗaya daga cikin bayin, ya tambaye shi abin da yake faruwa.

  10. Bawan ya ce, ‘Ai, ɗan’uwanka ne ya dawo, shi ne mahaifinka ya yanka ɗan saniya mai ƙiba, gama ya yi murna ya karɓi ɗansa da ya dawo gida lafiyayye, ba abin da ya same shi.’

  11. “Sai yayan ya yi fushi, ya ƙi shiga gida. Sai mahaifinsa ya fita ya roƙe shi.

  12. Amma ya amsa wa mahaifinsa ya ce, ‘Duba! Duk waɗannan shekaru, ina yin maka aiki kamar bawa, ban taɓa maka rashin biyayya ba. Duk da haka, ba ka taɓa ba ni ko ɗan akuya domin in yi shagali da abokaina ba.

  13. Amma da wannan ɗan naka, wanda ya ɓatar da dukiyarka a kan karuwai ya dawo, ka yanka masa ɗan saniya mai ƙiba!’

  14. “Sai mahaifin ya ce masa, ‘Ɗana, kullum kana nan tare da ni, kuma duk abin da nake da shi, naka ne.

  15. Amma ya zama mana dole, mu yi shagali, mu yi murna, domin ɗan’uwan nan naka, da ya mutu, yanzu kuwa yana da rai, da ya ɓata, amma yanzu an same shi.’ ”

  16. “Waɗansu mutane biyu sun tafi haikali don yin addu’a. Ɗaya Bafarisiye ne, ɗayan kuma mai karɓar haraji.

  17. Sai Bafarisiyen ya tashi tsaye, ya yi addu’a game da kansa yana cewa, ‘Allah, na gode maka, saboda ni ba kamar sauran mutane ba ne, wato, mafasa, masu aikata mugunta, masu zina, ko kuma kamar mai karɓar harajin nan.

  18. Ina azumi sau biyu a mako, ina ba da zakka daga kowane abin da na samu.’

  19. “Amma mai karɓar harajin ya tsaya daga nesa. Bai ma iya ɗaga kansa sama ba, sai ya buga ƙirjinsa, yana cewa, ‘Allah, ka yi mini jinƙai, ni mai zunubi ne.’

  20. “Ina gaya muku, wannan mutum ne, ba ɗayan ba, ya koma gida baratacce, babu laifi a gaban Allah. Gama duk wanda ya ɗaukaka kansa, za a ƙasƙantar da shi. Wanda kuma ya ƙasƙantar da kansa, za a ɗaukaka shi.”

  21. Saboda Ɗan Mutum ya zo ne, domin yă nemi abin da ya ɓata, yă cece shi kuma.”

  22. Duk waɗanda Uba ya ba ni za su zo wurina, kuma duk wanda ya zo wurina ba zan kore shi ba ko kaɗan.

  23. Ni ne ƙofar; duk wanda ya shiga ta wurina zai sami ceto. Zai riƙa shiga yă fita yă kuwa sami wurin kiwo.

  24. “Saboda haka, ’yan’uwana, ina so ku san cewa ta wurin Yesu ana sanar muku da gafarar zunubi.

  25. Ta wurinsa kowa da ya gaskata an kuɓutar da shi daga dukan abin da Dokar Musa ba tă iya kuɓutar ba.