Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Offence: The low station of Christ

7 ayoyi · 31 fannoni

Ayoyi game da The low station of Christ

  1. Wa ya gaskata saƙonmu kuma ga wa hannun Ubangiji ya bayyana?

  2. Ya yi girma kamar dashe marar ƙarfi, kamar saiwa kuma daga ƙeƙasasshiyar ƙasa. Ba shi da kyan gani ko wani makamin da zai ja hankalinmu, babu wani abin da yake da shi da zai sa mu yi sha’awarsa.

  3. Mutane suka rena shi suka ƙi shi, mutum ne cike da baƙin ciki, ya kuma saba da wahala. Kamar wanda mutane suna ɓuya fuskokinsu daga gare shi aka rena shi aka yi banza da shi.

  4. Yana isowa garinsa, sai ya fara koya wa mutane a cikin majami’arsu, suka kuwa yi mamaki. Suka yi ta tambaya suna cewa, “Ina wannan mutum ya sami irin wannan hikima da kuma ayyukan banmamaki haka?

  5. Wannan ba shi ne ɗan kafinta nan ba? Ba mahaifiyarsa ba ce Maryamu, ’yan’uwansa kuma Yaƙub, Yusuf, Siman da Yahuda ba?

  6. Duk ’yan’uwansa mata kuma ba tare da mu suke ba? To, a ina wannan mutum ya sami dukan waɗannan abubuwa?”

  7. Sai suka ji haushinsa. Amma Yesu ya ce musu, “Sai a garinsa da kuma a gidansa na kaɗai annabi ba ya samun girma.”