Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Offence: Punishment for occasioning

5 ayoyi · 31 fannoni

Ayoyi game da Punishment for occasioning

  1. Amma domin sun yi musu hidima a gaban gumakansu suka sa gidan Isra’ila ya yi zunubi, saboda haka na ɗaga hannu na rantse cewa dole su ɗauki alhakin zunubinsu, in ji Ubangiji Mai Iko Duka.

  2. Amma sai kuka kauce hanya, ta wurin koyarwarku kuma kuka sa mutane da yawa suka yi tuntuɓe; kun keta alkawarin da na yi da Lawi,” in ji Ubangiji Maɗaukaki.

  3. “Saboda haka na sa a rena ku, a kuma wulaƙanta ku a gaban dukan mutane, domin ba ku bi hanyoyina ba amma kuka nuna sonkai a al’amuran shari’a.”

  4. “Amma duk wanda ya sa ɗaya daga cikin ƙananan nan da suka gaskata da ni ya yi zunubi, zai fiye masa a rataya babban dutsen niƙa a wuyarsa, a kuma nutsar da shi a zurfin teku.

  5. Kaiton duniya saboda abubuwan da suke sa mutane su yi zunubi! Dole irin waɗannan abubuwa su zo, sai dai kaiton mutumin da ya zama sanadin kawo su!