Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Manna

57 ayoyi · 44 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Gama burodin Allah shi ne wanda yake saukowa daga sama, yana kuma ba wa duniya rai.”

  2. Sai suka ce, “Ranka yă daɗe, daga yanzu ka dinga ba mu wannan burodi.”

  3. Sa’an nan Yesu ya furta cewa, “Ni ne burodin rai. Wanda ya zo wurina ba zai taɓa jin yunwa ba, wanda kuma ya gaskata da ni ba zai taɓa jin ƙishirwa ba.

  4. Ni ne burodin rai.

  5. Kakannin-kakanninku sun ci Manna a hamada, duk da haka suka mutu.

  6. Amma ga burodin da ya sauko daga sama, wanda mutum zai iya ci, ba zai kuma mutu ba.

  7. Ni ne burodin rai mai saukowa daga sama. Duk wanda ya ci wannan burodi, zai rayu har abada. Wannan burodin shi ne jikina, da zan bayar don duniya ta sami rai.”