Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Macedonia

11 ayoyi · 6 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

  1. Sa’ad da hayaniyar ta kwanta, sai Bulus ya aika a kira almajiran, kuma bayan ya ƙarfafa su, sai ya yi bankwana ya tafi Makidoniya.

  2. Ya ratsa wurin yana ƙarfafa mutanen da kalmomi masu yawa, a ƙarshe kuma ya kai Giris,

  3. inda ya zauna wata uku. Da yake Yahudawa sun ƙulla masa makirci, a lokacin da yake shirin tashi cikin jirgin ruwa zuwa Suriya, sai ya yanka shawara yă koma ta Makidoniya.

  4. Sai Sofater ɗan Fairrus daga Bereya, Aristarkus da Sekundus daga Tessalonika, Gayus daga Derbe, Timoti ma, da Tikikus da Turofimus daga lardin Asiya suka tafi tare da shi.

  5. Waɗannan mutane suka sha gaba suka kuma jira mu a Toruwas.

  6. Amma muka tashi daga Filibbi a jirgin ruwa bayan Bikin Burodi Marar Yisti bayan kuma kwana biyar muka sadu da sauran a Toruwas, inda muka zauna kwana bakwai.

  7. To, ’yan’uwa, muna so ku san abin da alherin Allah ya ba wa ikkilisiyoyin Makidoniya.

  8. Gama sun sha wuya sosai saboda tsananin wahalar da suka shiga, har yawan farin cikinsu ya kai su ga yin alheri ta bayarwa ga waɗansu, ko da yake suna cikin tsananin talauci.

  9. Gama ina shaida cewa sun bayar daidai gwargwadon iyawarsu, har ma fiye da ƙarfinsu. Su kansu,

  10. sun roƙe mu sosai don su sami damar yin bayarwa a wannan hidima ga tsarkaka.

  11. Ba su yi yadda muka za tă ba, sai ma suka fara ba da kansu ga Ubangiji, sa’an nan sai suka ba da kansu gare mu bisa ga nufin Allah.