Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Kirjath-Jearim

63 ayoyi · 7 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Suka ɗauko akwatin alkawarin Allah a sabuwar keken yaƙi, suka kawo shi daga gidan Abinadab, wanda yake bisa tudu. Uzza da Ahiyo, ’ya’yan Abinadab maza, suka bi da keken yaƙin da akwatin alkawarin Allah yake ciki suka bi da keken yaƙin

  2. da akwatin alkawarin Allah yake ciki. Ahiyo kuwa yana tafiya a gaban Abinadab.

  3. Dawuda da dukan gidan Isra’ila suka yi biki sosai da dukan ƙarfinsu a gaban Ubangiji, da waƙoƙi, da molaye, da garayu, da ganguna, da kacau-kacau da kuma kuge.

  4. Da suka kai masussukar Nakon, sai Uzza ya miƙa hannu don yă riƙe akwatin alkawarin Allah, gama shanun sun yi tuntuɓe.

  5. Fushin Ubangiji kuwa ya ƙuna a kan Uzza domin aikin rashin bangirma, saboda haka Allah ya buge shi ya kuma mutu a can kusa da akwatin alkawarin Allah.

  6. Ran Dawuda ya ɓace gama fushin Ubangiji ya ɓarke a kan Uzza. Shi ya sa har wa yau ana kira wurin Ferez Uzza.

  7. Dawuda ya ji tsoron Ubangiji a ranar, sai ya ce, “Yaya akwatin alkawarin Ubangiji zai iya zuwa wurina?”

  8. Bai so yă ɗauki akwatin alkawarin Ubangiji yă kasance tare da shi a Birnin Dawuda ba. A maimakon haka sai ya kai shi gidan Obed-Edom mutumin Gat.

  9. Akwatin Alkawarin Ubangiji ya kasance a gidan Obed-Edom mutumin Gat har tsawon wata uku, Ubangiji kuwa ya albarkace shi da dukan iyalinsa.

  10. Saboda haka Dawuda ya tattara dukan Isra’ilawa, daga Kogin Shihor a Masar zuwa Lebo Hamat, don su kawo akwatin alkawarin Allah daga Kiriyat Yeyarim.

  11. Dawuda da dukan Isra’ilawa tare da shi suka tafi Ba’ala na Yahuda (Kiriyat Yeyarim) don su haura daga can su kawo akwatin alkawarin Allah Ubangiji, wanda yake zama tsakanin kerubobi, akwatin alkawarin da ake kira da Sunan.

  12. Suka ɗauki akwatin alkawarin Allah daga gidan Abinadab a kan sabon keken shanu, Uzza da Ahiyo ne suke lura da shi.

  13. Dawuda da dukan Isra’ilawa suka yi shagali da dukan ƙarfinsu a gaban Allah, tare da waƙoƙi da garayu, molaye, ganguna, kuge da ƙahoni.