Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Judges of Israel: The sons of Samuel

5 ayoyi · 17 fannoni

Ayoyi game da The sons of Samuel

  1. Da Sama’ila ya tsufa, sai ya naɗa ’ya’yansa maza su zama alƙalan Isra’ila.

  2. Sunan ɗansa na fari Yowel, na biyu kuwa Abiya. Suka yi alƙalanci a Beyersheba.

  3. Amma ’ya’yansa ba su bi hanyar mahaifinsu ba. Suka mai da hankalinsu ga neman kuɗi da cin hanci, suna kuma danne gaskiya.

  4. Sai dukan shugabannin Isra’ila suka taru suka zo wurin Sama’ila a Rama.

  5. Suka ce masa, “Ka tsufa, ’ya’yanka kuma ba sa bin hanyarka, saboda haka sai ka naɗa sarkin da zai bi da mu kamar yadda sauran ƙasashe suke da su.”