Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Homicide: Accidental

38 ayoyi · 12 fannoni

Ayoyi game da Accidental

Tace bisa littafi
  1. “In bijimi ya kashe namiji ko ta mace, dole a jajjefe bijimin har yă mutu, ba za a kuma ci namansa ba. Amma mai bijimin ba shi da laifi.

  2. In, har an san bijimin da wannan hali, an kuma yi wa mai shi gargaɗi, amma bai ɗaura shi ba, har ya kashe namiji ko ta mace, za a jajjefe bijimin tare da mai shi, har su mutu.

  3. Amma fa, in an bukace shi yă biya, zai biya don yă fanshi ransa ta wurin biyan abin da aka aza masa.

  4. Wannan doka ta shafi batun bijimin da ya kashe ɗa ko ’ya.

  5. In bijimin ya kashe bawa ko baiwa, mai shi zai biya shekel talatin na azurfa wa maigidan bawan, a kuma a jajjefe bijimin.

  6. ku zaɓi waɗansu garuruwan da za su zama biranen mafakarku, inda wanda ya kashe mutum cikin kuskure zai iya gudu zuwa.

  7. Za su zama wuraren mafaka daga hannun mai bin hakki, don kada a kashe mai kisankai, tun ba a kai shi gaban shari’a, a gaban taron jama’a ba.

  8. Waɗannan garuruwa shida da aka bayar za su zama biranen mafakarku.

  9. A ba da uku a wannan gefe na Urdun, a kuma ba da uku a Kan’ana, su zama biranen mafaka.

  10. Waɗannan garuruwa shida za su zama wurin mafaka wa Isra’ilawa, baƙi da duk sauran mutanen da suke zama a cikinsu, saboda duk wanda ya kashe mutum cikin kuskure yă iya gudu zuwa.

  11. “ ‘Amma in cikin tsautsayi ne ya soke shi, ba don ƙiyayya ba, ko kuma ya jefe shi, ba da gangan ba,

  12. ko kuwa bai gan shi ba, ya jefa dutsen da zai kashe shi a kansa, ya kuwa mutu, to, da yake shi ba abokin gābansa ba ne, bai kuma yi nufi yă ji masa ba,

  13. dole taro su yi hukunci tsakanin mai laifin, da mai bin hakkin jini bisa waɗannan ƙa’idodi.

  14. Dole taro su kāre wanda ake zargi da kisa, daga mai bin hakkin jini. Su mai da shi birnin mafaka inda ya gudu ya tafi. Dole yă kasance a can sai mutuwar babban firist, wanda aka shafe da mai mai tsarki.

  15. “ ‘Amma in wanda ake zargin ya kuskura ya fita, ya kai iyakar birnin mafaka wadda ya gudu ya je,

  16. idan mai bin hakkin jinin ya same shi a bayan gari, mai bin hakkin jinin zai iya kashe mai kisankai ɗin ba tare da wani laifi ba.

  17. Dole wanda ake zargin, yă kasance a birninsa na mafaka sai bayan mutuwa babban firist; sai bayan mutuwar babban firist ne kawai zai iya komo ga mallakarsa.

  18. Sa’an nan Musa ya keɓe birane uku gabas da Urdun,

  19. waɗanda duk wanda ya yi kisankai, in ba da gangan ba ne ya kashe maƙwabcinsa, wanda babu ƙiyayya tsakaninsu a dā, zai iya gudu zuwa. Zai iya gudu zuwa cikin ɗaya daga waɗannan birane, yă tsira da ransa.

  20. Biranen kuwa su ne, Bezer a dutsen hamada, don mutanen Ruben; Ramot Gileyad, don mutanen Gad; da kuma Golan a Bashan, don mutanen Manasse.

  21. sai ku keɓe wa kanku birane uku waɗanda suke a tsakiyar ƙasar da Ubangiji Allahnku yake ba ku ku mallaka.

  22. Ku gina hanyoyi zuwa cikinsu, ku kuma raba ƙasar da Ubangiji Allahnku yake ba ku gādo kashi uku, saboda duk wani da ya yi kisankai yă iya gudu zuwa can.

  23. Ga doka game da mutumin da ya kashe wani, ya kuma gudu don yă cece ransa, wani wanda ya kashe maƙwabcinsa ba da gangan ba, ba kuwa da wata ƙiyayya a tsakaninsu a dā ba.

  24. Misali, in mutum ya je jeji da maƙwabcinsa domin yankan itace, sai ruwan gatarinsa ya kwaɓe daga ƙotar yayinda yake saran itacen, ya sari maƙwabcin har ya mutu. Mutumin nan zai iya gudu zuwa ɗaya daga cikin waɗannan birane don yă ceci ransa.

  25. In ba haka ba mai neman ɗaukan fansa jini, zai iya binsa cikin fushi, yă cim masa, saboda nisan hanyar, har ya kashe shi, ko da yake bai cancanci mutuwa ba, tun da yake ba ƙiyayya tsakaninsa da abokinsa a dā.