Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Heir

39 ayoyi · 1 fanni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Sa’an nan ya ce wa dangin nan mai fansa, “Na’omi, wadda ta dawo daga Mowab, tana so ta sayar da filin da yake na ɗan’uwanmu Elimelek.

  2. Na ga ya kamata in jawo hankalinka ga batun in kuma ba da shawara ka saye shi a gaban waɗannan da suke zazzaune a nan da kuma a gaban dattawan jama’a. In kana so ka fanshe shi, to, sai ka yi. Amma in ba za ka yi ba, sai ka faɗa mini, don in sani. Gama babu wani mai izinin yin haka sai kai, ni ne kuwa na biye.” Sai ya ce, “Zan fansa.”

  3. Sa’an nan Bowaz ya ce, “A ranar da ka saya filin daga Na’omi da kuma daga Rut mutuniyar Mowab, ka sayi gwauruwar marigayin nan, domin ka riƙe sunan marigayin da kuma kayansa.”

  4. Da jin haka, sai dangin nan mai fansa ya ce, “To, ba zan iya fanshe shi ba don kada in yi wa nawa mallakar rauni. Za ka iya fanshe shi wa kanka. Ni dai ba zan iya ba.”

  5. (To, a kwanakin can a Isra’ila, domin a tabbatar da fansa da kuma musayar da mallaka, mutum zai cire takalminsa ya ba wa ɗayan. Wannan ita ce hanyar tabbatar da al’amarin a hukumance a cikin Isra’ila.)

  6. Saboda haka dangin nan mai fansa ya ce wa Bowaz, “Saye shi wa kanka.” Sai ya cire takalminsa.

  7. Sa’an nan Bowaz ya yi shela wa dattawa da kuma dukan mutane, “A yau ku ne shaidu cewa na saya daga Na’omi dukan mallakar Elimelek, Kiliyon da kuma Malon.

  8. Na kuma ɗauki Rut mutuniyar Mowab, gwauruwar Malon a matsayin matata domin sunan mamaci da kuma mallakarsa yă ci gaba, domin kada sunansa yă ɓace daga cikin iyali ko daga tarihin gari. A yau ku ne shaidu!”

  9. Sai dattawan da kuma dukan waɗanda suke a ƙofar suka ce, “Mu shaidu ne. Bari Ubangiji yă sa macen da take zuwa cikin gidanka ta zama kamar Rahila da Liyatu, waɗanda tare suka gina gidan Isra’ila. Bari ka sami martaba a cikin Efrata ka kuma zama sananne cikin Betlehem.

  10. Ta wurin ’ya’yan da Ubangiji zai ba ka ta wurin wannan mace, bari iyalinka yă zama kamar na Ferez, wanda Tamar ta haifa wa Yahuda.”

  11. Na ƙi jinin dukan abubuwan da na yi wahala ina yi a duniya, gama dole in bar su wa na bayana.

  12. Wa ya sani ko zai zama mai hikima ko kuma wawa? Duk da haka zai mallaki dukan aikin da na yi da ƙoƙarina da kuma dabarata a duniya. Wannan ma ba shi da amfani.

  13. Abin da nake nufi shi ne, muddin magāji yana ɗan yaro ne tukuna, babu bambanci tsakaninsa da bawa, ko da yake shi ne da mallakar kome.

  14. Yana ƙarƙashin iyayen goyonsa da masu riƙon amana har yă zuwa cikar lokacin da mahaifinsa ya sa.