Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Heart

30 ayoyi · 2 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Ku ƙaunaci Ubangiji Allahnku da dukan zuciyarku, da dukan ranku, da kuma dukan ƙarfinku.

  2. Waɗannan umarnai da nake ba ku a yau, za su kasance a zukatanku.

  3. Don mai bi da kaɗe-kaɗe. Ta Dawuda. Zabura ce. Ya Ubangiji, ka bincike ni ka kuwa san ni.

  4. Ka san sa’ad da na zauna da sa’ad da na tashi; ka san tunanina daga nesa.

  5. Ka san fitata da kuma kwanciyata; ka saba da dukan hanyoyina.

  6. Kafin in yi magana da harshena ka santa gaba ɗaya, ya Ubangiji.

  7. Ka kewaye ni, gaba da baya; ka sa hannunka a kaina.

  8. Irin wannan sanin game da ni ya fi ƙarfin magana, ya fi ƙarfi in gane.

  9. Ina zan tafi daga Ruhunka? Ina zan gudu in tafi daga gabanka?

  10. In na haura zuwa sammai, kana a can; in na yi gado a zurfafa, kana a can.

  11. In na tashi a fikafikan safiya, in na sauka a gefe mai nisa na teku,

  12. can ma hannunka zai bishe ni, hannunka na dama zai riƙe ni gam.

  13. In na ce, “Tabbatacce duhu zai ɓoye ni haske kuma zai zama dare kewaye da ni,”

  14. duhu ma ba zai zama duhu gare ka ba; dare zai haskaka kamar rana, gama duhu ya yi kamar haske gare ka.

  15. Zuciya mai farin ciki kan sa fuska tă yi haske, amma ciwon zuciya kan ragargaza rai.

  16. Zuciya mai la’akari kan nemi sani, amma bakin wawa wauta ce ke ciyar da shi.

  17. Dukan kwanakin mutumin da ake danniya fama yake yi, amma zuciya mai farin ciki yana yin biki kullum.

  18. Zuciya ta fi kome ruɗu ta fi ƙarfin warkewa. Wa zai iya gane ta?

  19. “Ni Ubangiji nakan bincike zuciya in gwada tunani, don in sāka wa kowane mutum bisa ga halinsa, bisa ga ayyukansa.”

  20. Zan ba su zuciya ɗaya in kuma sa sabon ruhu a cikinsu; zan fid da zuciyar dutse daga gare su in kuma ba su zuciya ta nama.

  21. Sa’an nan za su bi ƙa’idodina su kuma yi hankali ga kiyaye dokokina. Za su zama mutanena, ni kuwa zan zama Allahnsu.

  22. Amma game da waɗanda zukatansu suka karkata ga bin mugayen siffofi da gumakan banƙyama, zan sāka musu gwargwadon ayyukansu, in ji Ubangiji Mai Iko Duka.”

  23. Zan yayyafa muku ruwa mai tsabta, zan kuwa tsarkake ku daga dukan ƙazantarku daga kuma dukan gumakanku.

  24. Zan ba ku sabuwa zuciya in kuma sa sabon ruhu a cikinku; zan fid da zuciyar dutse in kuma ba ku zuciyar nama.

  25. Amma abubuwan da suke fitowa ta baki suna fitowa ne daga zuciya, su ne kuma suke ƙazantar da mutum.