Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Heart

30 ayoyi · 2 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Gama daga zuciya ne mugayen tunani, kisankai, zina, fasikanci, sata, shaidar ƙarya, ɓatan suna, suka fitowa.

  2. Waɗannan su ne suke ƙazantar da mutum; amma cin abinci ba tare da wanke hannuwa ba, ba ya ƙazantar da mutum.”

  3. Tabbatacce, sa’ad da Al’ummai, waɗanda ba su da dokar, suka aikata abubuwan da dokar take bukata, abubuwan sun zama doka ke nan gare su, ko da yake ba su da dokar.

  4. To, da yake sun nuna cewa abubuwan da dokar take bukata suna a rubuce a zukatansu, lamirinsu yana kuma ba da shaida, tunaninsu kuwa yanzu yana zarginsu ko kuma yana kāre su.

  5. Wannan zai faru a ranar da Allah ta wurin Yesu Kiristi zai shari’anta ɓoyayyun abubuwan da mutane suka yi, yadda bisharata ta furta.