- English
- King James KJV
- Complete Jewish CJB
- World English WEBM
- Berean Standard BSB
- American Standard ASV
- Geneva GNV
- Young's Literal YLT
- Douay-Rheims DRC
- International
- Shqip ALB
- العربية SVD
- বাংলা BN-IRV
- မြန်မာ Judson
- 简体文 CUV-S
- 繁體中文 CUV-T
- Čeština BKR
- Nederlands STVE
- Français LSG
- Deutsch SCH
- Ελληνικά Vamvas
- ગુજરાતી GU-IRV
- Hausa HCB
- עברית Hebrew
- हिन्दी HCV
- Magyar KAROLI
- Bahasa Indonesia INDO-TB
- Italiano Diodati
- 日本語 Kougo
- 한국어 Korean
- മലയാളം MAL
- मराठी MRCV
- Norsk DNB
- فارسی OPV
- Polski BG
- Português Almeida
- Română Cornilescu
- Русский Synodal
- Español RVG
- Kiswahili Neno
- Svenska SV1917
- Tagalog TAG-ADB
- தமிழ் TCV
- తెలుగు TSA
- ภาษาไทย THAI-KJV
- Українська Ohienko
- Tiếng Việt CADMAN
- Yorùbá YCB
Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Expediency
Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki
A matsayina na mai bin Ubangiji Yesu na tabbata ƙwarai cewa babu abincin da yake marar tsabta don kansa. Amma in wani ya ɗauka wani abu marar tsabta ne, to, a gare shi marar tsabta ne.
In kana ɓata wa ɗan’uwanka zuciya saboda abincin da kake ci, ba halin ƙauna kake nunawa ba ke nan. Kada abincin da kake ci yă zama hanyar lalatar da ɗan’uwanka wanda Kiristi ya mutu dominsa.
Kada ka bar abin da ka ɗauka a matsayi kyakkyawa yă zama abin zargi ga waɗansu.
Gama mulkin Allah ba batun ci da sha ba ne, sai dai na adalci, salama, da kuma farin ciki cikin Ruhu Mai Tsarki,
duk kuwa wanda yake bauta wa Kiristi a haka yana faranta wa Allah rai ne, yardajje kuma ga mutane.
Saboda haka sai mu yi iya ƙoƙari mu aikata abin da zai kawo salama da kuma ingantawa ga juna.
Kada ku lalatar da aikin Allah saboda abinci. Dukan abinci mai tsabta ne, sai dai ba daidai ba ne mutum yă ci abin da zai sa wani yă yi tuntuɓe.
Ya fi kyau kada ka ci nama ko ka sha ruwan inabi ko kuma ka yi wani abin da zai sa ɗan’uwanka yă fāɗi.
Bari duk ra’ayin da kake da shi game da wannan sha’ani yă kasance tsakaninka da Allah. Mai albarka ne wanda zuciyarsa ba tă ba shi laifi game da abin da shi da kansa ya ɗauka cewa daidai ne ba.
Gaskiya ne cewa ba ma samun yardar Allah ta wurin abin da muke ci. Ba ma rasa wani abu idan ba mu ci ba, kuma ba ma ƙaru da wani abu in muka ci.
Sai dai ku yi hankali, kada yin amfani da ’yancinku yă zama abin sa tuntuɓe ga marasa ƙarfi.
Gama in wani wanda lamirinsa ba shi da ƙarfi ya gan ka, kai da kake da wannan sani, kana ci a haikalin gumaka, ashe, ba zai sami ƙarfin halin cin abin da aka miƙa wa gumaka ba?
Saboda haka ta wurin sanin nan naka sai ka sa wannan ɗan’uwa marar ƙarfi wanda Kiristi ya mutu dominsa yă hallaka.
Sa’ad da ka rushe lamiri mai bi marar ƙarfi, ka yi wa Kiristi zunubi ke nan.
Saboda haka, in abin da nake ci zai sa ɗan’uwana yă yi zunubi, ba zan ƙara cin nama ba, don kada in sa shi yă yi tuntuɓe.
Ko da yake ina da ’yanci ba na kuma ƙarƙashin kowa, na mai da kaina bawa ga kowa, domin in rinjayi mutane da yawa.
Ga Yahudawa na zama kamar mutumin Yahuda, domin in rinjayi Yahudawa. Ga waɗanda suke ƙarƙashin doka kuma, na zama kamar wanda yake ƙarƙashin Dokar (ko da yake ni kaina ba na ƙarƙashin Doka), domin in rinjayi waɗanda suke ƙarƙashin Doka.
Ga waɗanda ba su da Dokar kuwa, na zama kamar wanda ba shi da Dokar (ko da yake ba ni da ’yanci daga dokar Allah, amma ina ƙarƙashin dokar Kiristi), domin in rinjayi waɗanda ba su da dokar.
Ga waɗanda ba su da ƙarfi, na zama marar ƙarfi, domin in rinjayi waɗanda ba su da ƙarfi. Na zama dukan abu ga dukan mutane, domin ko ta yaya in zai yiwu, in ceci waɗansu.
Ina yin dukan waɗannan ne saboda bishara, domin in sami rabo a cikin albarkarta.
“Ana da dama a yi kome” sai dai ba kome ba ne yake da amfani. “Ana da dama a yi kome” sai dai ba kome ba ne mai ginawa.
Kada wani yă kula da kansa kawai, sai dai yă kula da waɗansu kuma.
Ku ci kowane abin da ake sayarwa a kasuwar nama ba sai kun tambaya ba don kada lamiri yă damu da inda abin ya fito,
gama “Duniya da duk abin da yake cikinta na Ubangiji ne.”
In wani marar bi ya gayyace ku cin abinci kuka kuwa yarda ku je, sai ku ci ko mene ne da aka sa a gabanku, ba tare da tambaya don kada lamiri yă damu da inda abin ya fito.