Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Dishonesty

44 ayoyi · 1 fanni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. “In wani ya yi zunubi bai kuma yi aminci ga Ubangiji ba, wato, ta wurin yin wa abokin zamansa karya game da ajiyar da abokin ya ba shi amana, ko a kan wani alkawarin da suka yi wa juna, ko kuwa a kan yă cuci abokin,

  2. ko kuma idan ya sami abin da ya ɓace amma ya yi ƙarya cewa bai samu ba. Ko ya yi rantsuwar ƙarya a kan duk irin abubuwan da akan aikata na laifi,

  3. sa’ad da mutum ya yi irin laifin nan, ya kuwa tabbata mai laifi ne, to, sai yă komar da abin da ya ƙwace, ko abin da ya samu ta hanyar zalunci, ko abin da aka ba shi ajiya, ko abin da ya tsinta.

  4. Zai mai da abin da ya yi rantsuwar ƙarya a kai. Zai mayar wa mai abin da abinsa a yadda yake, har yă ƙara kashi ashirin bisa ɗari na abin. A ranar da zai yi hadaya don laifinsa, a ranar ce zai mayar wa mai abin da abinsa.

  5. A matsayin hakki kuwa, dole yă kawo wa firist, wato, ga Ubangiji, hadaya rago marar lahani kuma wanda aka kimanta tamaninsa daga garke don laifinsa.

  6. Ta haka firist zai yi kafara dominsa a gaban Ubangiji, za a kuwa gafarta masa irin laifin da ya yi.”

  7. “ ‘Kada ku yi amfani da mudun ƙarya sa’ad da kuke awon tsawo, nauyi, ko yawan abu.

  8. Ku yi amfani da ma’auni na gaskiya da mudu na gaskiya, da kuma magwaji na gaskiya. Ni ne Ubangiji Allahnku, wanda ya fitar da ku daga Masar.

  9. Kada ku kasance da ma’auni iri biyu a jakarku, ɗaya babba, ɗaya ƙarami.

  10. Kada ku kasance da mudu iri biyu a jakarku, ɗaya babba, ɗaya ƙarami.

  11. Dole ku kasance da ma’aunin da kuma mudun da yake daidai, kuma na gaskiya, saboda ku yi tsawon rai a ƙasar da Ubangiji Allahnku yake ba ku.

  12. Gama Ubangiji Allahnku yana ƙyamar duk mai yi waɗannan abubuwa, da kuma mai rashin gaskiya.

  13. Mugaye suna satar fili ta wurin matsar da duwatsun da aka yi iyaka da su; suna satar dabbobi su kuma yi kiwon su.

  14. Suna ƙwace wa marayu jakunansu suna kuma ƙwace wa gwauruwa sa don suna binta bashi.

  15. Suna ture matalauta daga hanya suna kuma sa dole matalautan ƙasar su ɓoye.

  16. Kamar jakunan jeji a hamada, matalauta suna aikin neman abinci gonaki marasa amfani suna tanada abinci wa ’ya’yansu.

  17. Suna girbi a gonakin da ba nasu ba, suna yin kala a gonar inabi ta mugaye.

  18. Don ba su da tufafi, sukan kwana tsirara; ba su da wani abin da zai rufe su cikin sanyi.

  19. Sun jiƙe sharkaf da ruwan da yake kwararowa daga duwatsu, sun rungume duwatsu don rashin wurin fakewa.

  20. Ana ƙwace jinjiri mai shan mama; ana ƙwace ɗan yaron matalauci don biyan bashi.

  21. Don ba su da tufafi suna yawo tsirara; suna dakon dammunan hatsi amma duk da haka suna cikin shan yunwa.

  22. Suna matse zaitun a cikin kunyoyi suna kuma matse ruwan inabi daga ’ya’yan inabi, duk da haka suna fama da ƙishi.

  23. Kada ka ƙi yin alheri ga duk wanda ya dace, sa’ad da kana iya yin haka.

  24. Kada ka ce wa maƙwabcinka “Ka yă dakata sai gobe,” idan kana iya taimakonsa yanzu.

  25. Amma ga shi, kuna dogara ga maganganu na ruɗami marasa amfani.