Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Decalogue

54 ayoyi · 5 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Sai Allah ya faɗi waɗannan kalmomi ya ce,

  2. “Ni ne Ubangiji Allahnka, wanda ya fitar da ku daga Masar, daga ƙasar bauta.

  3. “Ba za ka yi wa kanka waɗansu alloli ba sai ni.

  4. Ba za ka yi wa kanka waɗansu alloli a siffar wani abu a sama a bisa, ko a ƙarƙashin ƙasa, ko a ƙarƙashin ruwa ba.

  5. Ba za ka durƙusa gare su, ko ka yi musu sujada ba. Gama ni, Ubangiji Allahnka mai kishi ne, nakan hukunta ’ya’ya har tsara ta uku da ta huɗu na waɗanda suke ƙina,

  6. amma ina nuna ƙauna ga tsara dubbai na waɗanda suke ƙaunata, suke kuma kiyaye umarnaina.

  7. Ba za ka yi amfani da sunan Ubangiji Allahnka a banza ba, gama Ubangiji zai hukunta duk wanda ya mai da sunansa banza.

  8. Ka tuna da ranar Asabbaci domin ka kiyaye ta da tsarki.

  9. Kwana shida za ka yi dukan aikinka,

  10. amma rana ta bakwai Asabbaci ne ga Ubangiji, Allahnka. A ranar ba za ka yi wani aiki ba, ko kai, ko ɗanka, ko ’yarka, ko bawa, ko baiwa, ko dabbarka, ko baƙon da yake zama tare da kai.

  11. Gama kwana shida Ubangiji ya halicci sama da ƙasa, da teku, da duk abin da yake cikinsu, amma ya huta a rana ta bakwai. Saboda haka Ubangiji ya albarkaci ranar Asabbaci, ya kuma mai da ita mai tsarki.

  12. Ka girmama mahaifinka da mahaifiyarka, domin ka yi tsawon rai a ƙasar da Ubangiji Allahnka yake ba ka.

  13. Ba za ka yi kisankai ba.

  14. Ba za ka yi zina ba.

  15. Ba za ka yi sata ba.

  16. Ba za ka ba da shaidar ƙarya a kan maƙwabcinka ba.

  17. Ba za ka yi ƙyashin gidan maƙwabcinka ba. Ba za ka yi ƙyashin matar maƙwabcinka ba, ko bawansa, ko baiwarsa, ko sansa, ko jakinsa, ko duk abin da yake na maƙwabcinka ba.”

  18. Sa’an nan Ubangiji ya ce wa Musa, “Ka rubuta waɗannan kalmomi, gama bisa ga kalmomin nan, na yi alkawari da kai da kuma Isra’ila.”

  19. Musa ya kasance tare da Ubangiji kwana arba’in da dare arba’in, bai ci ba, bai sha ba. Ya kuma rubuta kalmomin alkawari a kan alluna, wato, dokoki goma.

  20. Ubangiji ya yi magana fuska da fuska da ku daga wuta a kan dutse.

  21. (A wannan lokaci na tsaya tsakanin Ubangiji da ku, don in furta muku maganar Ubangiji, domin kun ji tsoron wutar, ba ku kuwa hau dutsen ba.) Ya ce,

  22. “Ni ne Ubangiji Allahnka, wanda ya fitar da ku daga Masar, daga ƙasar bauta.

  23. “Ba za ka kasance da waɗansu alloli a gabana ba.

  24. Ba za ka yi wa kanka gunki, ko wata siffar abin da take a sama a bisa, ko siffar abin da yake a duniya a ƙasa, ko siffar abin da yake a cikin ruwa a ƙarƙashin ƙasa ba.

  25. Ba za ka rusuna musu, ko ka yi musu sujada ba. Gama Ni, Ubangiji Allahnka, Allah ne mai kishi, nakan hukunta ’ya’ya saboda zunuban iyaye har tsara ta uku da ta huɗu na waɗanda suka ƙi ni.