Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Creditor: Laws concerning

23 ayoyi · 3 fannoni

Ayoyi game da Laws concerning

  1. “In ka sayi mutumin Ibraniyawa a matsayin bawa, zai bauta maka shekara shida. Amma a shekara ta bakwai, za ka ’yantar da shi, yă tafi ’yantacce, ba tare da ya biya kome ba.

  2. In ya zo shi kaɗai, zai tafi ’yantacce shi kaɗai; amma in yana da mata a lokacin da ya zo, za tă tafi tare da shi.

  3. In maigidansa ya yi masa aure, ta kuwa haifa masa ’ya’ya maza ko mata, matan da ’ya’yan, za su zama na maigidan, sai mutumin kaɗai zai tafi ’yantacce.

  4. “Amma in bawan ya furta ya ce, ‘Ina ƙaunar maigidana, da matata, da ’ya’yana, ba na so kuma in ’yantu,’

  5. dole maigidansa yă kai shi gaban alƙalai. Zai kai shi ƙofa ko madogarar ƙofa, yă huda kunnensa da basilla, sa’an nan zai zama bawansa duk tsawon kwanakinsa a duniya.

  6. “In kun ba wa jama’ata matalauta da suke tsakaninku bashin kuɗi, kada ku zama kamar masu ba da rance; kada ku sa yă biya da ruwa.

  7. In kun ɗauki mayafi maƙwabcinku a matsayin jingina, ku mayar masa kafin fāɗuwar rana,

  8. domin mayafin ne abin da yake da shi na rufe jikinsa. To, da me zai rufu yă yi barci? Sa’ad da ya yi mini kuka, zan ji, gama ni mai tausayi ne.

  9. “ ‘In ka sayar da gona wa wani daga mutanen ƙasarka, ko ka saya wata gona daga gare shi, kada ku cuci juna.

  10. Sa’ad da mutum ya sayi fili daga abokin zamansa, kuɗin zai kasance bisa ga yawan shekara hamsin ta murna da suka wuce, da kuma bisa ga yawan shekarun noma da suka rage kafin wata shekara hamsin ta murna.

  11. Idan shekarun suna da yawa, sai ku kara kuɗin filin, idan kuma shekarun ba su da yawa, sai ku rage kuɗin filin, gama ainihin abin da ake sayar maka shi ne yawan hatsin.

  12. Kada ku cuci juna, amma ku ji tsoron Allahnku. Ni ne Ubangiji Allahnku.

  13. “ ‘In ɗaya daga ciki mutanen ƙasarku ya talauta, ba ya kuma iya tallafa wa kansa a cikinku, sai ku taimake shi kamar yadda za ku yi da baƙo a cikinku.

  14. Kada ku karɓi riba ta kowace iri daga gare shi, amma ku ji tsoron Allahnku, saboda mutumin ƙasarku yă ci gaba da zama a cikinku.

  15. Kada ku ba shi rancen kuɗi da ruwa, ko ku sayar masa abinci don samun riba.

  16. Ga yadda za ku yafe basusuwan, kowane mai bin bashi, yă yafe bashin da yake bin ɗan’uwansa mutumin Isra’ila. Ba zai bukaci mutumin Isra’ila wanda yake ɗan’uwa yă biya shi bashi ba, gama an yi shelar lokacin da Ubangiji ya ajiye na yafe bashi.

  17. Za ku iya nemi baƙo yă biya ku bashin da kuke binsa, amma dole ku yafe duk wani bashin da kuke bin ɗan’uwa.

  18. Kada ku nemi ɗan’uwanku yă biya bashin da kuka ba shi da ruwa, ko kuɗi, ko abinci, ko kowane irin abin da yana iya ba da ruwa.

  19. Za ku iya nemi ruwa a bashin da kuka ba baƙo, amma ba ɗan’uwanku mutumin Isra’ila ba, domin Ubangiji Allahnku yă sa muku albarka a kowane abin da kuka sa hannunku a kai, a ƙasar da kuke shiga ku ci gādonta.

  20. Sa’ad da kuka ba da rance na kowane iri ga maƙwabcinku, kada ku shiga gidansa don karɓar wani abu a matsayin jingina.

  21. Ku tsaya a waje ku bar mutumin da yake karɓan rancen yă kawo muku abin da zai bayar a matsayin jingina.

  22. In matalauci ne, kada ku kwana da abin da zai bayar a matsayin jingina a wurinku.

  23. Ku mayar da rigarsa a fāɗuwar rana saboda yă sami abin rufuwa. Yin haka zai sa yă gode muku, za a kuma ɗauka wannan a matsayin aikin adalci da kuka yi a gaban Ubangiji Allahnku.