Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Creditor: Merciful

8 ayoyi · 3 fannoni

Ayoyi game da Merciful

  1. “Saboda haka, mulkin sama yana kama da wani sarki wanda ya so yă yi ƙididdigar dukiyarsa da take a hannun bayinsa.

  2. Da ya fara ƙididdigar, sai aka kawo masa wani wanda yake bin bashin talenti dubu goma.

  3. Da yake bai iya biya ba, sai maigida ya umarta a sayar da shi da matarsa da yaransa da kuma duk abin da yake da shi, a biya bashin.

  4. “Bawan ya durƙusa a gabansa. Ya yi roƙo ya ce, ‘Ka yi mini haƙuri, zan biya ka ƙaf.’

  5. Maigidan bawan ya ji tausayinsa, ya yafe masa bashin, ya kuma sake shi.

  6. Yesu ya ce, “An yi waɗansu mutum biyu da suke riƙe bashin mai ba da rance. Ana bin guda dinari ɗari biyar, ɗayan kuma hamsin.

  7. Dukan biyun suka gagara biyansa, sai ya yafe musu. To, a ganinka, wa zai fi ƙaunar mutumin nan?”

  8. Siman ya amsa ya ce, “A ganina, wanda aka yafe wa mai yawa ne.” Sai Yesu ya ce, “Ka faɗa daidai.”