Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Court

29 ayoyi · 4 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Amma ka zaɓi mutane masu iyawa daga dukan mutane, maza masu tsoron Allah, amintattu, masu ƙin rashawa, ka sanya su shugabanni na dubbai, ɗari-ɗari, hamsin-hamsin da goma-goma.

  2. Bari waɗannan mutane su sassanta mutane a kan ƙananan matsaloli, amma kowace babban matsala, ko bukata ta musamman, sai su kawo wurinka, ƙananan matsaloli kuma sai su yanke hukuncin da kansu. Ta haka ne za su taimaka wajen ɗaukan nauyin jama’a, don su sa aikin yă zama maka da sauƙi.

  3. In ka yi haka, Allah ya umarta za ka iya jimre gajiyar, kuma dukan mutanen nan za su koma gida da murna.”

  4. Musa ya kasa kunne ga surukinsa, ya kuma aikata duk abin da ya faɗa.

  5. Ya zaɓi mutane masu iyawa daga cikin dukan Isra’ila, ya naɗa su shugabannin mutane, shugabanni a kan dubbai, ɗari-ɗari, hamsin-hamsin da goma-goma.

  6. Suka yi hidimar alƙalanci na mutane a dukan lokaci. Gardandamin da suke da wuya, suka kawo wurin Musa, amma ƙananan batuttuwa, suka shari’anta a tsakaninsu.

  7. Saboda haka na ɗauko shugabannin kabilanku masu hikima, waɗanda suka saba da ma’amala da jama’a, na sa su shugabanni a gabanku, waɗansu suka zama shugabanni a kan dubu-dubu, waɗansu a kan ɗari-ɗari, waɗansu a kan hamsin-hamsin, waɗansu kuma a kan goma-goma. Na sa su zama shugabanni a kabilanku.

  8. Na kuma umarci alƙalanku a wancan lokaci, na ce, “Ku yi adalci cikin shari’a tsakanin ’yan’uwanku, ko damuwar tana tsakanin ’yan’uwa Isra’ilawa ne, ko kuwa tsakanin Isra’ilawa da baƙin da suke zaune a cikinku.

  9. Kada ku nuna sonkai a cikin hukuncinku, ku saurari kowane ɓangare, babba da ƙarami, kada ku ji tsoron wani, gama hukunci na Allah ne. Ku kawo kowane batun da ya sha ƙarfinku, zan kuwa saurare shi.”

  10. In aka kawo ƙarar da yake da wuya sosai ga alƙali a kotunanku, ko wadda aka zub da jini ne, ko ta faɗa ce, ko kuwa ta wadda aka ci mutunci ce, ku kai su wurin da Ubangiji Allahnku zai zaɓa.

  11. Ku je wurin firistoci, waɗanda suke Lawiyawa, ga kuma alƙalin wanda yake mulki a lokacin. Ku bincika daga gare su, za su kuwa ba da hukunci.

  12. Dole ku aikata hukuncin da suka yi a wurin da Ubangiji zai zaɓa. Ku lura fa, ku aikata kome da suka faɗa muku.

  13. Ku yi bisa ga dokar da suka koyar muku da kuma hukuncin da suka yi muku. Kada ku juya daga abin da suka faɗa muku, ko zuwa dama, ko zuwa hagu.

  14. Duk mutumin da ya yi rashin hankali wa alƙali, ko ga firist wanda yake aiki a nan wa Ubangiji Allahnku, dole a kashe shi. Dole ku fid da mugu daga Isra’ila.

  15. Dukan mutane kuwa za su ji, su kuma ji tsoro, ba kuwa za su ƙara yin rashin hankali kuma ba.

  16. Sama’ila kuwa ya ci gaba da mulkin Isra’ila dukan rayuwarsa.

  17. Shekara-shekara Sama’ila yakan fita rangadi zuwa Betel, da Gilgal da Mizfa inda yakan yi musu shari’a.

  18. Amma yakan komo Rama inda gidansa yake, a nan yakan yi wa Isra’ila shari’a. A nan ne kuma ya gina wa Ubangiji bagade.

  19. Ya naɗa alƙalai a kowanne daga cikin biranen katanga na Yahuda a ƙasar.

  20. Ya faɗa musu, “Ku lura da abin da kuke yi, gama shari’ar da kuke yi ba ta mutum ba ce, amma ta Ubangiji ce, yana tare da ku sa’ad da kuke yanke shari’a.

  21. Yanzu fa ku ji tsoron Ubangiji. Ku yi hankali a kan abin da kuke yi, gama Ubangiji Allahnmu ba ya sonkai ko nuna wariya ko cin hanci.”

  22. A Urushalima kuma, Yehoshafat ya naɗa waɗansu Lawiyawa, firistoci da kawunan iyalan Isra’ilawa don su tabbatar da an bi dokar Ubangiji, su kuma sasanta tsakanin mutane. A Urushalima za su zauna.

  23. Ya ba su waɗannan umarnai, “Ku yi aikinku da aminci da tsoron Ubangiji da dukan zuciyarku.

  24. Cikin kowane batun da ya zo gabanku daga ’yan’uwanku waɗanda suke zama a birane, ko batun na kisa ne ko kuwa waɗansu batuttuwan da suka shafi doka, umarnai, ƙa’idodi ko farillai, dole ku ja musu kunne kada su yi wa Ubangiji zunubi; in ba haka ba fushinsa zai sauko a kanku da ’yan’uwanku. Ku yi wannan, ta haka ba za ku kuwa yi zunubi ba.

  25. Bulus ya zuba wa Majalisar ido ya ce, “’Yan’uwana, na cika aikina ga Allah cikin lamiri mai kyau har yă zuwa yau.”