Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Atonement

166 ayoyi · 2 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. “Sa’an nan zai yanka akuya na hadaya don zunubi saboda mutane, yă kai jinin bayan labule, yă yi da shi yadda ya yi da jinin bijimin. Zai yayyafa shi a kan murfin kafarar da kuma a gabansa.

  2. Ta haka zai yi kafara domin Wuri Mafi Tsarki saboda ƙazantar tawayen Isra’ilawa, da laifofinsu, da dukan zunubansu. Haka zai yi saboda Tentin Sujada wanda yake a cikinsu a tsakiyar ƙazantarsu.

  3. Kada kowa yă kasance a Tentin Sujada daga lokacin da Haruna ya shiga don yă yi kafara a Wuri Mafi Tsarki har sai ya fita, bayan ya yi kafara domin kansa, gidansa da kuma dukan jama’ar Isra’ila.

  4. “Sa’an nan zai fita zuwa bagade da yake a gaban Ubangiji, yă yi kafara dominsa. Zai ɗibi jinin bijimi da na akuya yă zuba a ƙahonin bagade.

  5. Zai yayyafa jinin a kan bagade da yatsarsa sau bakwai, yă tsabtacce shi yă kuma tsarkake shi daga ƙazantar Isra’ilawa.

  6. Zai yi wanka a tsattsarkan wuri yă sa rigunarsa na kullum. Sa’an nan zai fita yă miƙa hadaya ta ƙonawa domin kansa da hadaya ta ƙonawa domin mutane, don yă yi kafara domin kansa da kuma domin mutane.

  7. Zai kuma ƙone kitsen hadaya don zunubi a kan bagade.

  8. “Dole mutumin da ya saki akuya na azazel yă wanke rigunansa yă kuma yi wanka; bayan haka zai iya shiga sansani.

  9. Dole a ɗauki jini, fata, nama da kuma ƙashin bijimi da akuyan hadaya don zunubi, waɗanda aka kawo jininsu cikin Wuri Mafi Tsarki don kafara, a kai waje da sansani a ƙone.

  10. Dole mutumin da ya ƙone su yă wanke rigunansa yă kuma yi wanka, bayan haka zai iya shiga sansani.

  11. “Wannan za tă zama dawwammamiyar farilla a gare ku. A rana ta goma ga wata na bakwai, dole ku yi mūsu kanku, ba kuwa za ku yi wani aiki ba, ko da mutum baƙo ne a cikinku ko kuwa ɗan ƙasa,

  12. gama a wannan rana za a yi kafara dominku, don a tsarkake ku. Sa’an nan a gaban Ubangiji, za a tsarkake ku daga dukan zunubanku.

  13. Asabbaci ne don hutawa, kuma dole ku yi mūsun kanku; wannan dawwammamiyar farilla ce.

  14. Firist da aka keɓe aka kuma naɗa don yă gāji mahaifinsa a matsayin babban firist ne zai yi kafara. Zai sa rigunan lilin masu tsarki

  15. yă yi kafara domin Wuri Mafi Tsarki, Tentin Sujada da bagade, da kuma saboda firistoci da kuma dukan jama’ar Isra’ila.

  16. “Wannan za tă zama dawwammamiyar farilla ce gare ku. Za a riƙa yin kafara sau ɗaya a shekara saboda dukan zunuban Isra’ilawa.” Aka kuma yi haka, yadda Ubangiji ya umarci Musa.

  17. “ ‘To, in ku a matsayin jama’a, da gangan kuka ƙi kiyaye waɗannan ƙa’idodi da Ubangiji ya ba wa Musa ba,

  18. ko wani daga cikin umarnan da Ubangiji ya ba ku ta wurinsa, daga ranar da Ubangiji ya ba da su, har zuwa tsararraki masu zuwa,

  19. in kuwa aka yi haka ba da gangan ba, kuma da rashin sani, sai duk jama’a su miƙa ɗan bijimi don hadaya ta ƙonawa mai daɗin ƙanshi ga Ubangiji, tare da ƙayyadadden hadaya ta gari, da hadaya ta sha, da kuma bunsuru na hadaya don zunubi.

  20. Firist kuwa zai yi kafara domin dukan jama’ar Isra’ilawa, za a kuma gafarta musu, gama ba da gangan ba ne suka aikata, kuma sun kawo wa Ubangiji hadayar da akan yi da wuta da kuma hadaya don zunubi saboda laifinsu.

  21. Za a gafarta wa dukan jama’ar Isra’ilawa, da baƙin da suke zama a cikinsu, gama duk laifin da aka yi da rashin sani, yakan shafi dukan mutane.

  22. “ ‘Amma in mutum ɗaya ne kaɗai ya yi laifi ba da gangan ba, dole yă kawo akuya domin hadaya don zunubi.

  23. Firist zai yi kafara a gaban Ubangiji saboda mutumin nan da ya aikata laifi ba da gangan ba, in kuwa an yi kafara saboda shi, za a gafarta masa.

  24. kowane ’yan raguna bakwai, kashi ɗaya bisa goma.

  25. A haɗa da bunsuru guda a matsayin hadaya don zunubi, don yin muku kafara da kuma hadaya ta ƙonawa ta kullum; tare da hadaya ta garinta, da kuma hadayu na shansu.