Tsallake zuwa abun ciki

Beersheba

32 verses · 2 known names

An kuma san shi da: Beer-sheba

31.2400, 34.8400 Duba a Google Maps

Ayoyin da suka ambaci Beersheba

Tace bisa littafi
  1. Saboda haka Dawuda ya ce wa Yowab da shugabannin mayaƙa, “Ku tafi ku ƙidaya Isra’ilawa daga Beyersheba zuwa Dan. Ku kawo mini labarin saboda in san su nawa ne.”

  2. Yehoshafat ya zauna a Urushalima, ya kuma fita yana shiga cikin mutane daga Beyersheba zuwa ƙasar tudun Efraim ya kuma juyar da su ga Ubangiji Allah na kakanninsu.

  3. Yowash yana da shekara goma sha bakwai sa’ad da ya zama sarki, ya kuma yi sarauta a Urushalima shekara arba’in. Sunan mahaifiyarsa Zibiya ce; ita daga Beyersheba.

  4. Suka yanke shawara su yi shelar a ko’ina a Isra’ila, daga Beyersheba zuwa Dan, suna kiran mutane su zo Urushalima, suka kuma yi Bikin Ƙetarewa ga Ubangiji Allah na Isra’ila. Ba a yi bikin da mutane masu yawa bisa ga abin da aka rubuta ba.

  5. da Hazar Shuwal, da Beyersheba da ƙauyukanta.

  6. da Zanowa, da Adullam da ƙauyukansu, da Lakish da gonakinta, da kuma Azeka da ƙauyukanta. Saboda haka sun yi zama tun daga Beyersheba har zuwa Kwarin Hinnom.

  7. kada ku nemi Betel, kada ku je Gilgal, kada ku yi tafiya zuwa Beyersheba. Gama ba shakka Gilgal za tă tafi bauta, za a kuwa mai da Betel ba kome ba.”