Tsallake zuwa abun ciki

Saul

265 ayoyi · 11 'yan gida

Ayoyin da suka ambaci Saul

Tace bisa littafi
  1. Shawulu da Yonatan, a raye ƙaunatattu ne da kuma bansha’awa, a mace kuma ba su rabu ba. Sun fi gaggafa sauri, sun fi zaki ƙarfi.

  2. “Ya ku ’yan matan Isra’ila, ku yi kuka saboda Shawulu, wanda ya suturta ku da jajjayen kayan ado, wanda ya yi wa rigunarku ado da zinariya.

  3. Sa’an nan mutanen Yahuda suka zo Hebron, a can kuwa suka naɗa Dawuda sarkin Yahuda. Sa’ad da aka gaya wa Dawuda cewa mutanen Yabesh Gileyad ne suka binne Shawulu,

  4. sai ya aiki manzanni zuwa Yabesh Gileyad a ce musu, “Ubangiji yă albarkace ku saboda alherin da kuka nuna wa Shawulu ta wurin binne shi.

  5. Yanzu fa, sai ku ƙarfafa, ku yi jaruntaka, gama Shawulu sarkinku ya mutu, gidan Yahuda kuwa sun naɗa ni sarki a kansu.”

  6. Ana cikin haka, Abner ɗan Ner, komandan sojojin Shawulu, ya ɗauki Ish-Boshet ɗan Shawulu ya kawo shi Mahanayim.

  7. Ish-Boshet ɗan Shawulu yana da shekaru arba’in sa’ad da ya zama sarkin Isra’ila, ya kuma yi sarauta shekara biyu. Amma fa, gidan Yahuda, suka bi Dawuda.

  8. Dawuda ya ce, “Da kyau, zan yi yarjejjeniya da kai, amma fa ina bukata abu guda daga gare ka, kada ka zo gabana in ba tare da matata Mikal, ’yar Shawulu ba.”

  9. Sai Dawuda ya aiki manzanni zuwa wurin Ish-Boshet ɗan Shawulu cewa, “Ka ba ni matata Mikal wadda na biya sadakinta da loɓa ɗari na Filistiyawa.”

  10. Sa’ad da Ish-Boshet ya ji labari cewa Abner ya mutu a Hebron, sai ya karaya, sai dukan hankalin Isra’ila ya tashi.

  11. To, ɗan Shawulu yana da ’ya’ya maza biyu da suke shugabannin ’yan hari. Ana kiran ɗaya Ba’ana, ɗayan kuma Rekab. Su ’ya’yan Rimmon mutumin Benyamin ne daga Beyerot, an lissafta Beyerot a ɓangaren Benyamin,

  12. (Yonatan ɗan Shawulu yana da ɗa mai suna Mefiboshet wanda yake gurgu a duka ƙafafu. Yana da shekara biyar ne sa’ad da labarin mutuwar Shawulu da Yonatan ya zo daga Yezireyel. Sai mai renonsa ta ɗauke shi ta gudu, amma yayinda take hanzari tă gudu, sai ya fāɗo, ya gurgunce.)

  13. Sa’ad da akwatin alkawarin Ubangiji ya shiga Birnin Dawuda, sai Mikal ’yar Shawulu ta leƙa ta taga ta ga Dawuda sarki yana tsalle, yana rawa a gaban Ubangiji, sai ta rena shi a zuciyarta.

  14. Sai sarki ya kira Ziba bawan Shawulu, ya ce masa, “Na ba wa jikan maigidanka kome da yake na Shawulu da iyalinsa

  15. suna da baka suna kuma iya harba kibiya, ko majajjawa da hannun dama ko na hagu; su ’yan’uwan Shawulu ne daga kabilar Benyamin):