God
Ayoyin da suka ambaci God
“Ɗan mutum, ’yan’uwanka, ’yan’uwanka waɗanda suke danginka na cikinka da kuma dukan gidan Isra’ila su ne waɗanda mutanen Urushalima suka ce, ‘Su ne da nisa daga Ubangiji; an ba mu wannan ƙasa ta zama mallakarmu.’
“Saboda haka ka ce, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa ko da yake na kore su zuwa cikin al’ummai na kuma warwatsa su cikin ƙasashe, duk da haka na zama wuri mai tsarki a gare su a ƙasashen da suka tafi.’
“Saboda haka, ka ce, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa zan tattaro ku daga al’ummai in kuma dawo da ku daga ƙasashen da aka warwatsa ku, zan kuwa sāke mayar muku da ƙasar Isra’ila.’
Zan ba su zuciya ɗaya in kuma sa sabon ruhu a cikinsu; zan fid da zuciyar dutse daga gare su in kuma ba su zuciya ta nama.
Sa’an nan za su bi ƙa’idodina su kuma yi hankali ga kiyaye dokokina. Za su zama mutanena, ni kuwa zan zama Allahnsu.
Amma game da waɗanda zukatansu suka karkata ga bin mugayen siffofi da gumakan banƙyama, zan sāka musu gwargwadon ayyukansu, in ji Ubangiji Mai Iko Duka.”
Sa’an nan kerubobi, tare da da’irori kusa da su, suka buɗe fikafikansu, ɗaukakar Allah kuwa tana a bisansu.
Ɗaukakar Ubangiji ta haura daga cikin birnin ta sauka a bisa dutse gabas da shi.
Ruhu ya ɗaga ni sama ya kuma kawo ni ga masu zaman bauta a ƙasar Babilon cikin wahayin da Ruhun Allah ya bayar. Sa’an nan wahayin da na gani ya rabu da ni,
na kuwa faɗa wa masu zaman bautan dukan abin da Ubangiji ya nuna mini.
Maganar Ubangiji ta zo mini cewa
Ka sa su a kafaɗarka yayinda suke kallo ka kuma fitar da su da dare. Ka rufe fuskarka don kada ka ga ƙasar, gama na mai da kai alama ga gidan Isra’ila.”
Da safe maganar Ubangiji ta zo mini cewa,
“Ka ce musu, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa wannan abin da Allah ya yi magana a kai ya shafi sarki a Urushalima da kuma dukan gidan Isra’ila waɗanda suke a can.’
Ka ce musu, ‘Ni alama ne a gare ku.’ “Kamar yadda na yi, haka za a yi da su. Za a kai su zaman bauta kamar kamammu.
Zan shimfiɗa masa ragata, za a kuwa kama shi da tarkona; zan kawo shi Babiloniya, ƙasar Kaldiyawa, amma ba zai gan ta ba, a can kuwa zai mutu.
Zan warwatsa dukan waɗanda suke kewaye da shi a dukan fuskokin iska, ma’aikatansa da dukan rundunoninsa, zan fafare su da takobin da aka zāre.
“Za su san cewa ni ne Ubangiji sa’ad da na watsar da su a cikin al’ummai na kuma warwatsa su cikin ƙasashe.
Amma zan bar kaɗan daga cikinsu su tsere wa takobi, yunwa da annoba, saboda a cikin al’umman da suka tafi su furta dukan ayyukansu masu banƙyama. Sa’an nan za su san cewa ni ne Ubangiji.”
Maganar Ubangiji ta zo mini cewa,
Ka faɗa wa mutanen ƙasar cewa, ‘Ga abin Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa game da waɗanda suke zama a Urushalima da kuma cikin ƙasar Isra’ila. Za su ci abincinsu da razana, su sha ruwansu da tsoro, gama za a washe dukan abin da yake ƙasarsu saboda hargitsin dukan waɗanda suna zama a can.
Garuruwan da mutane suna ciki za su zama kufai ƙasar kuma za tă zama kango. Sa’an nan za ku san cewa ni ne Ubangiji.’ ”
Maganar Ubangiji ta zo mini cewa,
Ka ce musu, ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa zan kawo ƙarshen wannan karin magana, ba za su ƙara faɗar wannan karin magana a Isra’ila ba.’ Ka ce musu, ‘Kwanaki sun gabato da za a tabbatar da kowane wahayi.
Amma Ni Ubangiji zan yi magana abin da na nufa, za tă kuwa tabbata ba tare da jinkiri ba. Gama cikin kwanakinku, kai gidan ’yan tawaye, zan cika duk abin da na faɗa, in ji Ubangiji Mai Iko Duka.’ ”