Skip to content
Ƙidaya 10:11-36

Ƙidaya 10:11-36

11
A rana ta ashirin ga wata na biyu, a shekara ta biyu, sai girgijen ya tashi daga tabanakul na Shaida.
12
Sai Isra’ilawa suka tashi daki-daki daga Hamadar Sinai, suna tafiya daga wuri zuwa wuri, har sai da girgijen ya tsaya a Hamadar Faran.
13
Suka kama hanya, a wannan lokaci, bisa umarnin Ubangiji, ta wurin Musa.
14
Ɓangarorin sansanin Yahuda suka fara tashi, bisa ga ƙa’idar da aka yi, aka kuma umarta. Nashon ɗan Amminadab ne shugaba.
15
Netanel ɗan Zuwar ne shugaban ɓangaren kabilar Issakar,
16
Eliyab ɗan Helon kuma shi ne shugaban ɓangaren kabilar Zebulun.
17
Sa’an nan aka saukar da tabanakul ƙasa, Gershonawa da mutanen Merari da suke ɗauke da shi suka kama hanya.
18
Sai ɓangarori sansanin Ruben suka biyo, bisa ga ƙa’idar da aka yi, aka kuma umarta. Elizur ɗan Shedeyur ne shugaba.
19
Shelumiyel ɗan Zurishaddai ne shugaban ɓangaren kabilar Simeyon,
20
Eliyasaf ɗan Deyuwel kuma shi ne shugaban ɓangaren kabilar Gad.
21
Sai Kohatawa suka kama hanya, ɗauke da kayayyaki masu tsarki, domin kafin su kai wurin da za a kafa sansani, a riga an kafa tabanakul.
22
Biye da waɗannan kuma sai ɓangaren sansanin kabilar Efraim suka biyo bisa ga ƙa’ida da aka yi, aka kuma umarta. Elishama ɗan Ammihud ne shugaba.
23
Gamaliyel ɗan Fedazur ne shugaban ɓangaren kabilar Manasse,
24
Abidan ɗan Gideyoni kuma shi ne shugaban ɓangaren kabilar Benyamin.
25
A ƙarshe, a matsayi masu gadin bayan dukan ɓangarori, sai ɓangaren sansanin Dan suka tashi bisa ga ƙa’idar da aka yi, aka kuma umarta. Ahiyezer ɗan Ammishaddai ne shugaba.
26
Fagiyel ɗan Okran ne shugaban ɓangaren kabilan Asher,
27
Ahira ɗan Enan kuma shi ne shugaban kabilar Naftali.
28
Wannan shi ne tsarin tafiyar ɓangarorin Isra’ilawa, sa’ad da sukan kama hanya.
29
Sai Musa ya ce wa Hobab ɗan Reyuwel Bamidiyane surukinsa, “Yanzu fa, muna shirin tashi ne daga nan, domin mu tafi inda Ubangiji ya ce, ‘Zan ba ku.’ Ka zo tare da mu, za mu kuwa yi maka alheri, gama Ubangiji ya yi wa Isra’ilawa alkawari abubuwa masu kyau.”
30
Ya amsa, ya ce “A’a, ba zan tafi ba; zan koma ƙasata da kuma wurin mutanena.”
31
Amma Musa ya ce, “Ina roƙonka kada ka rabu da mu. Ka san inda ya kamata mu kafa sansani a hamada, za ka kuma zama idanunmu.
32
In ka zo tare da mu, za mu raba duk abin alherin Ubangiji ya ba mu tare da kai.”
33
Saboda haka suka kama hanya daga dutsen Ubangiji, suka yi tafiya kwana uku. Akwatin alkawarin Ubangiji ya ja gabansu a waɗannan kwanaki uku, don yă samo musu masauƙi.
34
A duk lokacin da suka tashi daga sansani, girgijen Ubangiji ya inuwantar da su da rana.
35
Duk kuma sa’ad da akwatin ya kama hanya, sai Musa ya ce, “Ka tashi, ya Ubangiji! Ka sa maƙiyanka su warwatse; masu ƙinka kuma su gudu a gabanka.”
36
Duk sa’ad da akwatin ya sauka kuma, sai Musa ya ce, “Ka komo, ya Ubangiji, a wurin dubban da ba a iya ƙidayawa na iyalan Isra’ila.”
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options