Skip to content
Ƙidaya 10:1-10

Ƙidaya 10:1-10

1
Ubangiji ya ce wa Musa,
2
“Ka ƙera kakaki guda biyu na azurfa, ka kuma yi amfani da su don kira taron jama’a wuri ɗaya, don kuma ka riƙa sanar da su lokacin tashi daga sansani.
3
Sa’ad da aka busa su biyu, dukan jama’a za su taru a gabanka a ƙofar Tentin Sujada.
4
In ɗaya ne kaɗai aka busa, sai shugabannin kabilan Isra’ila, su taru a gabanka.
5
Sa’ad da aka ji karar busar kakaki, sai sansanin da yake a gabashi, su kama hanya.
6
A kara ta biyu, sansanin da yake a kudanci, su kama hanya. Busan kakaki zai zama alama ta kama hanya.
7
In don a tara jama’a ne, sai a busa kakaki, amma ba da irin alama ɗaya ba.
8
“’Ya’yan Haruna, firistoci ne, za su busa kakaki. Wannan za tă zama dawwammamiyar farilla gare ku da kuma tsararraki masu zuwa.
9
Duk lokacin da za ku tafi yaƙi a ƙasarku, in akwai waɗansu da suke matsa muku, za ku yi amfani da waɗannan kakaki ta wurin hura su, alama ce, cewa za a je yaƙi. Sa’an nan Ubangiji Allahnku zai tuna da ku, yă cece ku daga maƙiyanku.
10
Haka ma in kuna cikin jin daɗinku, musamman lokacin da kuke bukukkuwanku, kamar Bikin Sabon Wata da dai kowane Bikinku, za ku hura waɗannan kakaki lokacin da kuke miƙa hadayunku na ƙonawa, da hadayunku na salama, za su kuma zama muku abin tunawa a gaban Allahnku. Ni ne Ubangiji Allahnku.”
Settings

Reading Style

Typeface

Font Size 19px

Options