Skip to content
Mattiyu 22:23-46

Mattiyu 22:23-46

23
A ranan nan Sadukiyawa, waɗanda suke cewa babu tashin matattu, suka zo wurinsa da tambaya.
24
Suka ce “Malam, Musa ya faɗa mana cewa in mutum ya mutu ba shi da ’ya’ya, dole ɗan’uwansa yă auri gwauruwar yă kuma haifar wa ɗan’uwan ’ya’ya.
25
A cikinmu an yi ’yan’uwa guda bakwai. Na fari ya yi aure, ya mutu, da yake bai sami ’ya’ya ba, sai ya bar matarsa wa ɗan’uwansa.
26
Haka ya faru da ɗan’uwa na biyu da na uku, har zuwa na bakwai.
27
A ƙarshe, macen ta mutu.
28
To, a tashin matattu, matar wa a cikinsu bakwai ɗin nan za tă zama, da yake dukansu sun aure ta?”
29
Yesu ya amsa ya ce, “Kun ɓata, domin ba ku san Nassi ko ikon Allah ba.
30
Ai, a tashin matattu, mutane ba za su yi aure ko su ba da aure ba; za su zama kamar mala’iku a sama.
31
Amma game da tashi daga matattu na waɗanda suka mutu ba ku karanta abin da Allah ya ce muku ba ne,
32
‘Ni ne Allah na Ibrahim, Allah na Ishaku da kuma Allah na Yaƙub’? Ai, shi ba Allah na matattu ba ne, shi Allah na masu rai ne.”
33
Da taro suka ji haka, sai suka yi mamakin koyarwarsa.
34
Da jin Yesu ya ƙure Sadukiyawa, sai Farisiyawa suka tattaru.
35
Ɗaya daga cikinsu, wani masanin Doka, ya gwada shi da wannan tambaya.
36
“Malam, wace doka ce mafi girma a cikin dokoki?”
37
Yesu ya amsa ya ce, “ ‘Ka ƙaunaci Ubangiji Allahnka da dukan zuciyarka da dukan ranka da kuma dukan hankalinka.’
38
Wannan, ita ce doka ta fari da kuma mafi girma.
39
Ta biye kuma kamar ta farkon take. ‘Ka ƙaunaci maƙwabcinka kamar kanka.’
40
Dukan Doka da Annabawa suna rataya ne a kan waɗannan dokoki biyu.”
41
Yayinda Farisiyawa suke a tattare wuri ɗaya, sai Yesu ya tambaye su,
42
“Me kuke tsammani game da Kiristi? Ɗan wane ne shi?” Suka amsa suka ce, “Ɗan Dawuda.”
43
Ya ce musu, “To, ta yaya Dawuda ya yi magana ta wurin Ruhu Mai Tsarki, ya kira shi ‘Ubangiji’? Gama ya ce,
44
“ ‘Ubangiji ya ce wa Ubangijina, “Zauna a hannun damana, sai na sa abokan gābanka su zama matashin sawunka.” ’
45
To, in Dawuda ya kira shi ‘Ubangiji,’ yaya zai zama ɗansa?”
46
Ba wanda ya iya tanka masa, daga wannan rana kuwa ba wanda ya sāke yin karambanin yin masa wata tambaya.
Settings

Reading style

Typeface

Font size 19px

Reading width 75 chars

Options