Skip to content
Luka 23:35-56

Luka 23:35-56

35
Mutanen suka tsaya suna kallo. Har masu mulki ma suka yi masa ba’a, suna cewa, “Ya ceci waɗansu, to, ya ceci kansa in shi ne Kiristi na Allah, Zaɓaɓɓe.”
36
Sojoji su ma, suka zo suka yi masa ba’a. Suka miƙa masa ruwan tsami.
37
Suka ce, “In kai ne sarkin Yahudawa, ka ceci kanka mana.”
38
Bisa da shi kuma akwai rubutun da ya ce, Wannan shi ne Sarkin Yahudawa.
39
Ɗaya daga cikin masu laifin da aka gicciye a wurin ya zazzage shi ya ce, “Shin, ba kai ne Kiristi ba? To, ka ceci kanka, ka kuma cece mu mana!”
40
Amma ɗayan mai laifi ya kwaɓe shi ya ce, “Ba ka da tsoron Allah ne, wai saboda kana ƙarƙashin hukunci ɗaya tare da shi?
41
Horonmu, daidai aka yi mana, sakamakon abin da muka yi ne. Amma wannan mutum, bai yi wani laifi ba.”
42
Sai ya ce, “Yesu, ka tuna da ni sa’ad da ka shiga mulkinka.”
43
Yesu ya amsa, ya ce masa, “Gaskiya nake faɗa maka, yau ɗin nan, za ka kasance tare da ni, a mulkina a sama.”
44
Yanzu kuwa wajen sa’a ta shida ne, kuma duhu ya rufe ko’ina a ƙasar, har zuwa sa’a ta tara,
45
domin rana ta daina haskakawa. Labulen da yake cikin haikali kuma ya yage kashi biyu.
46
Yesu ya yi kira da babbar murya ya ce, “Ya Uba, na danƙa ruhuna a hannunka.” Da ya faɗi haka, sai ya ja numfashi na ƙarshe.
47
Da jarumin ya ga abin da ya faru, sai ya yabi Allah ya ce, “Gaskiya, wannan mutum mai adalci ne.”
48
Da dukan mutanen da suka taru, domin shaidar waɗannan abubuwa, suka ga abin da ya faru, sai suka buga ƙirjinsu suka tafi.
49
Amma dukan mutanen da suka san Yesu, tare da mata da suka bi shi daga Galili, suka tsaya daga nesa suna kallon abubuwan nan.
50
Akwai wani mutum mai suna Yusuf, ɗan Majalisa, wanda shi nagari ne, mai adalci,
51
shi dā ma bai yarda da shawararsu, da kuma abin da suka yi ba. Shi daga Arimateya ne wani garin Yahudiya. Yana kuma jiran zuwa mulkin Allah.
52
Sai ya je wurin Bilatus ya roƙa a ba shi jikin Yesu.
53
Sai ya saukar da jikin, ya nannaɗe shi a cikin zanen lilin, ya sa shi a wani kabari da aka fafe a cikin dutse, wadda ba a taɓa sa kowa ba.
54
An yi haka ne a Ranar Shirye-shirye, ranar Asabbaci kuma yana dab da farawa.
55
Matan da suka zo tare da Yesu, daga Galili suka bi Yusuf suka ga kabarin, da kuma yadda aka ajiye jikin.
56
Sa’an nan, suka koma gida, suka shirya kayan ƙanshi da turare. Amma suka huta a ranar Asabbaci don kiyaye doka.
Settings

Reading style

Typeface

Font size 19px

Reading width 75 chars

Options