Skip to content
Luka 22:6-30

Luka 22:6-30

6
Ya ko yarda, ya fara neman zarafin da zai ba da Yesu a gare su, sa’ad da taro ba sa nan tare da shi.
7
Sai ranar Bikin Burodi Marar Yisti ta kewayo, wato, ranar hadayar ɗan ragon kafara na Bikin Ƙetarewa.
8
Sai Yesu ya aiki Bitrus da Yohanna, ya ce musu, “Ku je ku yi shirye-shiryen Bikin Ƙetarewar da za mu ci.”
9
Suka tambaye shi suka ce, “Ina kake so mu je mu yi shirin?”
10
Ya amsa ya ce, “Sa’ad da kuka shiga cikin gari, za ku sadu da wani mutum yana ɗauke da tulun ruwa. Ku bi shi zuwa gidan da zai shiga.
11
Ku ce wa maigidan, Malam ya aike mu mu ce maka, ‘Ina ɗakin baƙi, inda ni da almajiraina za mu ci abincin Bikin Ƙetarewa?’
12
Zai nuna muku wani babban ɗakin sama a shirye. Nan za ku yi shirin.”
13
Sai suka tafi, suka kuma iske kome kamar yadda Yesu ya faɗa musu. Sai suka shirya Bikin Ƙetarewa.
14
Da lokaci ya yi, sai Yesu ya zauna tare da manzanninsa don cin abinci.
15
Sai ya ce musu, “Na yi marmari ƙwarai don in ci wannan Bikin Ƙetarewa tare da ku, kafin in sha wahala.
16
Ina dai gaya muku, ba zan ƙara cinsa ba, sai ya sami cika a mulkin Allah.”
17
Bayan ya ɗauki kwaf ruwan inabi, ya yi godiya, sai ya ce, “Ku karɓa, ku rarraba wa junanku.
18
Ina dai gaya muku, ba zan ƙara sha daga ’ya’yan inabi ba, sai mulkin Allah ya zo.”
19
Sai ya ɗauki burodi ya yi godiya, ya kakkarya ya ba su, da cewa, “Wannan jikina ne, da aka bayar dominku. Ku riƙa yin haka don tunawa da ni.”
20
Haka kuma, bayan abincin, ya ɗauki kwaf ruwan inabi ya ce, “Wannan kwaf ruwan inabi shi ne, na sabon alkawari cikin jinina, da aka zubar dominku.
21
Amma hannun wanda zai ci amanata, yana cin abincin tare da ni.
22
Ɗan Mutum zai mutu kamar yadda aka ƙaddara, amma kaiton mutumin da zai bashe shi.”
23
Sai suka fara tambayar junansu, ko wane ne a cikinsu zai yi wannan.
24
Gardama ta tashi a tsakaninsu, a kan ko wane ne a cikinsu ya fi girma.
25
Yesu ya ce musu, “Sarakunan Al’ummai suna nuna iko a kan mutanensu, kuma waɗanda suke nuna iko a kansu, suna kiran kansu Masu Taimakon mutane.
26
Amma ku, kada ku zama haka. A maimakon haka, sai dai wanda ya fi girma a cikinku, ya zama kamar wanda ya fi ƙanƙanta, wanda kuma ke mulki, ya zama kamar mai hidima.
27
Wane ne ya fi girma? Wanda yake zaune a tebur ne, ko kuma shi da yake yin hidima? Ashe, ba wanda yake zaune a tebur ba ne? Amma ga ni, ni mai yin hidima ne a cikinku.
28
Ku ne kuka tsaya tare da ni a gwaje-gwajen da na sha.
29
Daidai kamar yadda Ubana ya ba ni mulki, haka ni ma nake ba ku.
30
Saboda ku ci, ku sha a teburina a cikin mulkina. Kuma ku zauna a kan gadon sarauta, ku yi wa kabilu goma sha biyu na Isra’ila shari’a.
Settings

Reading style

Typeface

Font size 19px

Reading width 75 chars

Options