Skip to content
Yohanna 16:1-18

Yohanna 16:1-18

1
“Na faɗa muku wannan duka, domin kada ku bauɗe.
2
Za su kore ku daga majami’a; lalle, lokaci yana zuwa da duk wanda ya kashe ku, zai ɗauka yana yin wa Allah hidima ne.
3
Za su yi waɗannan abubuwa ne domin ba su san Uba ko ni ba.
4
Na faɗa muku wannan, domin in lokacin ya yi, ku tuna na gargaɗe ku. Ban faɗa muku wannan tun da fari ba domin ina tare da ku.
5
“Yanzu zan tafi wurin wanda ya aiko ni, duk da haka ba waninku da ya tambaye ni, ‘Ina za ka?’
6
Saboda na faɗa waɗannan abubuwa ga shi kun cika da baƙin ciki.
7
Amma gaskiya nake gaya muku. Don amfaninku ne zan tafi. Sai ko na tafi, in ba haka ba Mai Taimakon nan ba zai zo muku ba. Amma in na tafi, zan aiko shi gare ku.
8
Sa’ad da ya zo kuwa, zai kā da duniya a kan zunubi da adalci da kuma hukunci,
9
a kan zunubi, domin mutane ba su gaskata da ni ba;
10
a kan adalci, domin zan tafi wurin Uba, inda ba za ku ƙara ganina ba;
11
a kan hukunci kuma, domin an yanke hukunci a kan mai mulkin duniyan nan.
12
“Ina da sauran abubuwa da yawa da zan faɗa muku, amma ba za ku iya ɗauka a yanzu ba.
13
Amma sa’ad da shi, Ruhun gaskiya ya zo, zai bi da ku zuwa ga dukan gaskiya. Ba zai yi magana don kansa ba; zai faɗi abin da ya ji ne kaɗai, zai kuma faɗa muku abin da bai faru ba tukuna.
14
Zai kawo ɗaukaka gare ni ta wurin ɗaukan abin da yake nawa, ya bayyana muku.
15
Duk abin da yake na Uba nawa ne. Shi ya sa na ce, ‘Ruhun zai ɗauko daga abin da yake nawa, yă bayyana muku.’ ”
16
Yesu ya ci gaba da cewa, “Jim kaɗan, ba za ku ƙara ganina ba, sa’an nan bayan an jima kaɗan kuma, za ku gan ni.”
17
A nan fa sai waɗansu almajiransa suka ce wa juna, “Me yake nufi da cewa, ‘Jim kaɗan ba za ku ƙara ganina ba, kuma bayan an jima kaɗan, za ku gan ni,’ da kuma, ‘Domin zan tafi wurin Uba’?”
18
Suka yi ta tambaya, “Me yake nufi da ‘jim kaɗan’? Ba mu fahimci abin da yake faɗi ba.”
Settings

Reading style

Typeface

Font size 19px

Reading width 75 chars

Options