Yohanna 16:25-33
25
“Ko da yake ina magana da misalai, lokaci yana zuwa da ba zan ƙara yin magana da misalai ba, sai dai in faɗa muku a fili game da Ubana.
26
A ranan nan, za ku roƙa a cikin sunana. Ban ce zan roƙi Uba a madadinku ba.
27
Ai, shi Uban kansa yana ƙaunarku domin kun ƙaunace ni kun kuma gaskata cewa daga Allah na fito.
28
Na fito daga wurin Uba, na kuma shigo duniya, yanzu kuwa zan bar duniya in koma wurin Uba.”
29
Sai almajiran Yesu suka ce, “Haba, yanzu ne fa kake magana a sarari ba tare da misalai ba.
30
Yanzu mun gane cewa ka san kome ba sai wani ya tambaye ka ba. Wannan ya sa muka gaskata ka fito daga Allah.”
31
Yesu ya amsa ya ce, “A ƙarshe kun gaskata!
32
Amma lokaci na zuwa, har ma ya yi, da za a warwatsa ku, kowa yă koma gidansa. Za ku bar ni ni kaɗai. Duk da haka ba ni kaɗai ba ne, gama Ubana yana tare da ni.
33
“Na faɗa muku waɗannan abubuwa ne, domin a cikina ku sami salama. A duniyan nan za ku sha wahala. Amma ku yi ƙarfin hali! Na yi nasara a kan duniya.”
Settings