Farawa 31:24-42
24
Sai Allah ya bayyana ga Laban mutumin Aram a mafarki da dare, ya ce masa, “Ka yi hankali kada ka faɗa wa Yaƙub wani abu, ko mai kyau ko marar kyau.”
25
Yaƙub ya riga ya kafa tentinsa a yankin tuddan Gileyad sa’ad da Laban ya same shi. Laban da danginsa suka kafa sansani a can su ma.
26
Sai Laban ya ce wa Yaƙub, “Me ke nan ka yi? Ka ruɗe ni, ka kuma ɗauki ’ya’yana mata kamar kamammun yaƙi.
27
Me ya sa ka gudu a ɓoye ka kuma ruɗe ni? Me ya sa ba ka faɗa mini don in sallame ka da farin ciki da waƙoƙi haɗe da kiɗin ganguna da garayu ba?
28
Ba ka ma bari in sumbaci jikokina da ’ya’yana mata in yi musu bankwana ba. Ka yi wauta.
29
Ina da iko in cuce ka; amma jiya da dare Allahn mahaifinka ya faɗa mini, ‘Ka yi hankali kada ka faɗa wa Yaƙub wani abu ko mai kyau ko marar kyau.’
30
Yanzu ka gudu domin kana marmari komawa gidan mahaifinka. Amma don me ka sace mini gumakana?”
31
Yaƙub ya amsa wa Laban, “Na ji tsoro ne, domin na yi tsammani za ka ƙwace ’ya’yanka mata daga gare ni ƙarfi da yaji.
32
Amma in ka sami wani wanda yake da gumakanka, ba zai rayu ba. Kai da kanka ka duba a gaban danginmu, ko akwai wani abin da yake naka a nan tare da ni; in ka gani, ka ɗauka.” Yaƙub dai bai san cewa Rahila ta sace gumakan ba.
33
Saboda haka Laban ya shiga tentin Yaƙub, ya shiga tentin Liyatu da kuma tentuna matan nan biyu bayi, amma bai sami kome ba. Bayan ya fita daga tentin Liyatu, sai ya shiga tentin Rahila.
34
Rahila fa ta kwashe gumakan gidan ta sa su cikin sirdin raƙumi, ta kuma zauna a kansu. Laban ya bincika cikin kowane abu a tentin amma bai sami kome ba.
35
Sai Rahila ta ce wa mahaifinta, “Kada ka yi fushi, ranka yă daɗe da ban tashi tsaye a gabanka ba; gama ina al’adar mata ne.” Saboda haka ya bincika amma bai sami gumakan gidan ba.
36
Yaƙub ya fusata, ya kuma yi wa Laban faɗa. Ya tambayi Laban, “Mene ne laifina? Wanda zunubi na yi da kake farautata?
37
Yanzu da ka bincika dukan kayayyakina, me ka samu da yake na gidanka? Kawo shi nan a gaban danginka da kuma dangina, bari su zama alƙali tsakaninmu biyu.
38
“Na kasance tare da kai shekaru ashirin. Tumakinka da awakinka ba su yi ɓarin ciki ba, ban kuwa ci raguna daga garkunanka ba.
39
Ban kawo dabbobinka da namun jeji suka yayyaga; na kuma ɗauki hasarar ba? Ka nemi in biya dukan abin da aka sace da rana ko da dare.
40
Yanayin da na kasance ke nan, da rana na sha zafin rana da dare kuma na sha sanyi, ga rashin barci.
41
Haka ya kasance shekaru ashirin da na yi a gidanka. Na yi maka aiki shekaru goma sha huɗu domin ’ya’yanka mata biyu, na kuma yi shekaru shida domin garkunanka, ka kuma canja albashina sau goma.
42
Da ba don Allah na mahaifina, Allah na Ibrahim da kuma Tsoron Ishaku ya kasance tare da ni ba, tabbatacce da ka sallame ni hannu wofi. Amma Allah ya ga wahalata da famar hannuwana, ya kuwa tsawata maka da dare jiya.”
Settings