Skip to content
Ezekiyel 16:49-63

Ezekiyel 16:49-63

49
“ ‘To, fa, ga zunubin ’yar’uwarki Sodom. Ita da ’ya’yanta mata sun yi girman kai, sun ƙoshi fiye da kima kuma ba su kula da wani abu ba; ba su taimaki matalauta da kuma masu bukata ba.
50
Su masu girman kai ne kuma suka aikata abubuwa masu banƙyama a gabana. Saboda haka na kau da su kamar yadda ka gani.
51
Samariya ba tă aikata ko rabin zunubanki ba. Kin aikata abubuwa masu banƙyama fiye da su, suka kuma sa ’yan’uwanki mata suka zama kamar masu adalci ta wurin dukan waɗannan abubuwa da kika aikata.
52
Ki sha kunyarki, gama kin yi rangwame wa ’yan’uwanki mata. Saboda zunubanki sun yi muni fiye da nasu, sai suka zama kamar sun fi ki adalci. Saboda haka, ki sha kunya ki kuma sha ƙasƙancinki, gama kin sa ’yan’uwanki mata suka zama kamar su masu adalci ne.
53
“ ‘Amma fa, zan komo da nasarar Sodom da ’ya’yanta mata da ta Samariya da ’ya’yanta mata, nasararki kuma tare da su,
54
domin ki sha ƙasƙancinki ki kuma sha kunyar dukan abin da kika aikata ta wurin ta’azantar da su.
55
’Yan’uwanki kuwa, Sodom da ’ya’yanta mata da Samariya tare da ’ya’yanta mata, za su koma kamar yadda suke a dā; ke kuma da ’ya’yanki mata za ku koma kamar yadda kike a dā.
56
Ba za ki ma iya ambaci ’yar’uwarki Sodom a ranar fariyarki ba,
57
kafin a tone muguntarki. Ko da ma haka, yanzu ’ya’yan Arameyawa mata da dukan maƙwabtanta da kuma ’ya’yan Filistiyawa mata suna miki dariyar, dukan waɗanda suke kewaye da ke da suka rena ki.
58
Za ki ɗauki hakkin lalatarki da kuma ayyukanki masu banƙyama, in ji Ubangiji.
59
“ ‘Ga abin da Ubangiji Mai Iko Duka yana cewa zan hukunta kamar yadda ya dace da ke, domin kin ƙyale rantsuwana ta wurin karya alkawari.
60
Duk da haka zan tuna da alkawarin da na yi da ke a kwanakin ƙuruciyarki, zan kuma kafa madawwamin alkawari da ke.
61
Sa’an nan za ki tuna da hanyoyinki ki kuma ji kunya sa’ad da kika karɓi ’yan’uwanki mata, waɗanda suka girme ki da kuma waɗanda kika girme su. Zan ba da su kamar ’ya’ya mata gare ki, amma ba bisa alkawarina da ke ba.
62
Ta haka zan kafa alkawarina da ke, za ki kuma san cewa ni ne Ubangiji.
63
Sa’an nan, sa’ad da na yi kafara saboda ke domin dukan abin da kika aikata, za ki tuna ki kuma ji kunya har ki kāsa buɗe bakinki saboda kunya, in ji Ubangiji Mai Iko Duka.’ ”

Rubutun Littafi Mai Tsarki: Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™, © 2009, 2020 Biblica, Inc. · CC BY-SA 4.0“Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc., used with permission.

Settings

Reading style

Typeface

Font size 19px

Reading width 75 chars

Options