Skip to content
Fitowa 2:11-22

Fitowa 2:11-22

11
Wata rana, bayan Musa ya yi girma, sai ya haura, ya tafi inda mutanensa suke, ya kuma ga yadda suke shan wahala da aiki. Ya ga wani mutumin Masar yana dūkan mutumin Ibraniyawa, ɗaya daga cikin mutanensa.
12
Da ya leƙa nan da can bai kuwa ga kowa ba, sai ya kashe mutumin Masar, ya ɓoye shi a yashi.
13
Kashegari ya fita, sai ya ga Ibraniyawa biyu suna faɗa. Ya tambayi mai laifin ya ce, “Don me kake bugun ɗan’uwanka, mutumin Ibraniyawa?”
14
Mutumin ya ce masa, “Wa ya mai da kai mai mulki da mai hukunci a kanmu? Kana so ne ka kashe ni kamar yadda ka kashe mutumin Masar nan?” Sai Musa ya tsorata, ya yi tunani ya ce, “To, fa, abin nan da na yi, ya zama sananne.”
15
Da Fir’auna ya ji wannan, sai ya yi ƙoƙari yă kashe Musa, amma Musa ya gudu daga wajen Fir’auna, ya tafi ƙasar Midiyan inda ya zauna kusa da wata rijiya.
16
To, fa, akwai wani firist na Midiyan, yana da ’ya’ya mata bakwai, suka zo su shayar da dabbobin mahaifinsu.
17
Sai waɗansu makiyaya suka zo suka kore su, amma Musa ya tashi ya taimake su ya shayar da dabbobinsu.
18
Da ’yan matan suka komo wurin Reyuwel mahaifinsu, sai ya tambaye su ya ce, “Yaya kuka dawo da wuri yau?”
19
Suka amsa suka ce, “Wani mutumin Masar ne ya taimake mu daga hannun waɗansu makiyaya. Har ma ya ɗebo ruwa ya shayar da dabbobin.”
20
Ya tambayi ’yan matansa, “To ina yake? Don me kuka bar shi a can? A gayyace shi, yă zo, yă ci wani abu.”
21
Musa ya yarda yă zauna da mutumin wanda ya ba da ’yarsa Ziffora aure da Musa.
22
Ziffora ta haifi wa Musa ɗa, ya kuma raɗa masa suna Gershom cewa, “Na zama baƙo a baƙuwar ƙasa.”

Rubutun Littafi Mai Tsarki: Biblica® Open Hausa Contemporary Bible™, © 2009, 2020 Biblica, Inc. · CC BY-SA 4.0“Biblica” is a trademark registered in the United States Patent and Trademark Office by Biblica, Inc., used with permission.

Settings

Reading style

Typeface

Font size 19px

Reading width 75 chars

Options