Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Worship: Of Abraham
Ayoyi game da Of Abraham
Ubangiji ya bayyana ga Abram ya ce, “Ga zuriyarka ne zan ba da wannan ƙasa.” Saboda haka Abram ya gina bagade a can ga Ubangiji, wanda ya bayyana gare shi.
Daga can, ya ci gaba zuwa wajen tuddai a gabashin Betel ya kafa tentinsa, Betel yana yamma, Ai, kuma a gabas. A can ya gina bagade ga Ubangiji ya kuma kira bisa sunan Ubangiji.
da kuma inda dā ya gina bagade. A can Abram ya kira bisa sunan Ubangiji.
Saboda haka Abram ya cire tentunansa, ya zo ya zauna kusa da manyan itatuwan Mamre a Hebron, inda ya gina bagade ga Ubangiji.