Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Vineyard: Parables of

43 ayoyi · 9 fannoni

Ayoyi game da Parables of

Tace bisa littafi
  1. Zan rera waƙa wa ƙaunataccena waƙa game da gonar inabinsa. Ƙaunataccena yana da gonar inabi a gefen tudu mai dausayi.

  2. Ya haƙa ƙasa ya kuma tsintsince duwatsun ya shuka mata inabi mafi kyau. Ya gina hasumiyar tsaro a cikinta ya kuma shirya wurin matsin ruwan inabi. Sa’an nan ya sa rai ga samun girbi mai kyau na inabin, amma sai ga shi inabin ya ba da munanan ’ya’ya.

  3. “Yanzu fa ku mazauna cikin Urushalima da mutanen Yahuda, ku shari’anta tsakanina da gonar inabina.

  4. Me kuma ya rage da za a yi wa gonar inabina fiye da abin da na yi mata? Da na nemi inabi masu kyau, me ya sa ta ba da munana ’ya’ya?

  5. Yanzu zan faɗa muku abin da zan yi da gonar inabina. Zan cire katangar da ta kewaye ta, za tă kuwa lalace; zan rushe bangonta, za a kuwa tattake ta.

  6. Zan mai da ita kango, ba zan aske ta ba, ba kuwa zan nome ta ba, sarƙaƙƙiya da ƙayayyuwa kuwa za su yi girma a can Zan umarci gizagizai kada su yi ruwan sama a kanta.”

  7. Gonar inabin Ubangiji Maɗaukaki ita ce gidan Isra’ila, mutanen Yahuda kuma su ne lambun farin cikinsa. Yana kuma nema ganin gaskiya, amma sai ga zub da jini; yana neman adalci, amma sai ga shi kukan azaba yake ji.

  8. A wannan rana, “Ku rera game da gonar inabi mai ba da ’ya’ya ku ce

  9. Ni, Ubangiji na lura da ita; na yi ta yin mata banruwa. Na yi tsaronta dare da rana don kada wani yă yi mata ɓarna.

  10. Makiyaya masu yawa za su lalace gonar inabina su tattake gonata; za su mai da gonata mai kyau kango marar amfani.

  11. “Mulkin sama yana kama da wani mai gona, wanda ya fita da sassafe don yă yi hayar mutane su yi aiki a gonar inabinsa.

  12. Ya yarda yă biya su dinari guda a yini, sai ya tura su gonar inabinsa.

  13. “Wajen sa’a ta uku, ya fita sai ya ga waɗansu suna tsattsaye a bakin kasuwa ba sa kome.

  14. Ya ce musu, ‘Ku ma ku tafi gonar inabina ku yi aiki, zan kuwa biya ku abin da ya dace.’

  15. Saboda haka suka tafi. “Ya sāke fita a sa’a ta shida da kuma sa’a ta tara, ya sāke yin haka.

  16. Wajen sa’a ta goma sha ɗaya, ya sāke fita, ya tarar da waɗansu har yanzu suna tsattsaye. Ya tambaye su, ‘Don me kuke yini tsattsaye a nan ba kwa kome?’

  17. “Suka amsa, ‘Don ba wanda ya ɗauke mu aiki.’ “Ya ce musu, ‘Ku ma ku je ku yi aiki a gonar inabina.’

  18. “Sa’ad da yamma ta yi, sai mai gonar inabin ya ce wa wakilinsa, ‘Kira ma’aikatan, ka biya su hakkin aikinsu, fara daga waɗanda aka ɗauke su a ƙarshe har zuwa na farko.’

  19. “Ma’aikatan da ka ɗauka wajen sa’a ta goma sha ɗaya suka zo, kowannensu kuwa ya karɓi dinari guda.

  20. Saboda haka da waɗanda aka ɗauka da fari suka zo, sun zaci za su sami fiye da haka. Amma kowannensu ma ya karɓi dinari guda.

  21. Sa’ad da suka karɓa, sai suka fara yin gunaguni a kan mai gonar.

  22. Suna cewa, ‘Waɗannan mutanen da aka ɗauka a ƙarshe sun yi aikin sa’a ɗaya ne kawai, ka kuma mai da su daidai da mu da muka yini muna faman aiki, muka kuma sha zafin rana.’

  23. “Amma ya amsa wa ɗayansu ya ce, ‘Aboki, ban cuce ka ba. Ba ka yarda ka yi aiki a kan dinari guda ba?

  24. Ka karɓi hakkinka ka tafi. Ni na ga damar ba waɗannan na ƙarshe daidai da yadda na ba ka.

  25. Ba ni da ikon yin abin da na ga dama da kuɗina ne? Ko kana kishi saboda ni mai kyauta ne?’