Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Treasure: Money

8 ayoyi · 6 fannoni

Ayoyi game da Money

  1. Yusuf ya yi umarni a cika buhunansu da hatsi, a kuma sa azurfan kowane mutum a cikin buhunsa, a kuma ba su kalaci don tafiyarsu. Bayan aka yi musu wannan,

  2. A wurin da suka tsaya don su kwana, ɗaya daga cikinsu ya buɗe buhunsa don yă ciyar da jakinsa, sai ya ga azurfansa a bakin buhunsa.

  3. Sai ya ce wa ’yan’uwansa, “An mayar mini da azurfata. Ga shi a cikin buhuna.” Zuciyarsu ta karai, suka dubi juna suna rawan jiki, suka ce, “Mene ne wannan da Allah ya yi mana?”

  4. Yayinda suke juyewa hatsi daga buhunansu, sai ga ƙunshin azurfan kowane mutum a buhunsa! Sa’ad da su da mahaifinsu suka ga ƙunshe-ƙunshen kuɗi, suka firgita.

  5. Mutanen dai suka firgita sa’ad da aka ɗauke su zuwa gidansa. Suka yi tunani, “An kawo mu nan ne saboda azurfan da aka sa a cikin buhunanmu da farko. Yana so yă fāɗa mana, yă kuma sha ƙarfinmu, yă ƙwace mu kamar bayi, yă kuma kwashe jakunanmu.”

  6. amma a inda muka tsaya don mu kwana, da muka buɗe buhunanmu sai kowannenmu ya sami azurfansa daidai a bakin buhunsa. Saboda haka ga kuɗin a hannunmu, mun sāke komowa da su.

  7. Mun kuma kawo ƙarin azurfa tare da mu don mu saya abinci. Ba mu san wa ya sa azurfanmu a cikin buhunanmu ba.”

  8. Sai mai hidimar ya ce, “Ba kome, kada ku ji tsoro. Allahnku, Allahn mahaifinku ne ya ba ku dukiyar a cikin buhunanku; ni dai, na karɓi azurfanku.” Sa’an nan ya fitar musu da Simeyon.