Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da The Trinity: Inspiring the prophets, &c
Ayoyi game da Inspiring the prophets, &c
Sa’ad da aka kama ku, aka kuma kai ku don a yi muku shari’a, kada ku damu da abin da za ku faɗa. Sai dai ku faɗi abin da aka ba ku a lokacin. Gama ba ku kuke magana ba, Ruhu Mai Tsarki ne.
da yake kuna neman tabbaci cewa Kiristi yana magana ta wurina ne. To, ai, shi ba rarrauna ba ne a gare ku, amma ƙaƙƙarfa ne a cikinku.
A dā Allah ya yi wa kakanni-kakanninmu magana ta bakin annabawa a lokuta dabam-dabam da kuma a hanyoyi iri-iri,