Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da The Happiness of the Wicked

24 ayoyi · 25 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

  1. Haman ya fita a ranan da murna, ya kuma ji daɗi. Amma sa’ad da ya ga Mordekai a bakin ƙofar sarki, ya kuma lura cewa bai tashi, ko yă nuna bangirma a gabansa ba, sai ya cika da fushi.

  2. Duk da haka, Haman ya cije, ya tafi gida. Sai ya kira abokansa da kuma matarsa, Zeresh,

  3. ya yi ta taƙama game da ɗumbun wadatarsa, da yawan ’ya’yansa maza, da dukan yadda sarki ya girmama shi, ya kuma ɗaga shi bisan sauran hakimai da shugabanni.

  4. sai da na shiga wuri mai tsarki na Allah; sa’an nan na gane abin da ƙarshensu zai zama.

  5. Tabbatacce ka sa su a ƙasa mai santsi; ka jefar da su ga hallaka.

  6. Duba yadda suka hallaka farat ɗaya, razana ta share su gaba ɗaya!

  7. Kamar yadda mafarki yake sa’ad da mutum ya farka, haka yake sa’ad da ka farka, ya Ubangiji, za ka rena su kamar almarai.

  8. Zan kawar da muryoyin farin ciki da murna daga gare su, muryoyin amarya da na ango, ƙarar dutsen niƙa da hasken fitila.

  9. Dukan wannan ƙasa za tă zama kango, kuma waɗannan al’ummai za su bauta wa sarkin Babilon shekaru saba’in.

  10. Sai ya gaya musu wannan misali ya ce, “Gonar wani mai arziki ta ba da amfani sosai.

  11. Ya yi tunani a ransa ya ce, ‘Ba ni da inda zan ajiye amfanin gonana. Me zan yi ke nan?’

  12. “Sai ya ce, ‘Ga abin da zan yi. Zan rushe rumbunana, in gina manya, in zuba dukan hatsina da kayana a ciki.

  13. Ni kuma zan ce wa raina, “Kana da kaya da yawa masu kyau, da aka yi ajiyarsu domin shekaru da dama masu zuwa. Yi hutunka, ka ci, ka sha, ka yi annashuwa.” ’

  14. “Amma Allah ya ce masa, ‘Kai wawa! A wannan dare za a nemi ranka. Bayan haka, wa zai gāji abin da ka tara wa kanka?’

  15. “An yi wani mutum mai arziki wanda yakan sa tufafi masu ruwan shunayya, da kuma na lallausan lilin, yana kuma cikin rayuwar jin daɗi kullum.

  16. A ƙofar gidansa kuma akan ajiye wani mai bara, mai suna Lazarus, wanda jikinsa duk gyambuna ne.

  17. Shi kuwa yakan yi marmarin cin abin da yakan fāɗi daga tebur na mai arzikin nan. Har karnuka ma sukan zo su lashe gyambunansa.

  18. “Ana nan, sai mai baran ya mutu, kuma mala’iku suka ɗauke shi zuwa gefen Ibrahim. Mai arzikin ma ya mutu, aka kuma binne shi.

  19. A cikin jahannama ta wuta, inda yana shan azaba, ya ɗaga kai ya hangi Ibrahim can nesa, da kuma Lazarus a gefensa.

  20. Sai ya yi masa kira ya ce, ‘Baba, Ibrahim, ka ji tausayina, ka aiki Lazarus ya sa ɗan yatsarsa a ruwa, ya ɗiga mini a harshe saboda in ji sanyi, domin ina shan azaba cikin wannan wuta.’

  21. “Amma Ibrahim ya ce, ‘Ka tuna fa ɗana, a lokacin da kake duniya, ka sami abubuwa masu kyau naka, Lazarus kuwa ya sami munanan abubuwa. Amma yanzu ya sami ta’aziyya a nan, kai kuwa kana shan azaba.

  22. A ranar da aka shirya Hiridus, sanye da kayan sarautarsa, ya zauna a gadon sarautarsa ya kuma ya wa mutanen jawabi.

  23. Suka tā da murya suka ce, “Wannan muryar wani allah ne, ba ta mutum ba.”

  24. Nan take, domin Hiridus bai yi wa Allah yabo ba, wani mala’ikan Ubangiji ya buge shi, tsutsotsi kuwa suka cinye shi ya kuma mutu.