Skip to content

Zeresh

3 ayoyi · 1 ɗan gida

Ayoyin da suka ambaci Zeresh

  1. Duk da haka, Haman ya cije, ya tafi gida. Sai ya kira abokansa da kuma matarsa, Zeresh,

  2. Matarsa Zeresh, da dukan abokansa suka ce masa, “Ka sa a gina wurin rataye mai laifi, mai tsawo, ƙafa saba’in da biyar, da safe kuwa ka ce wa sarki a rataye Mordekai a kansa. Sa’an nan ka tafi cin abincin dare tare da sarki da murna.” Wannan shawarar ta faranta wa Haman rai, ya kuma sa aka gina wurin rataye mai laifi.

  3. Ya je ya faɗa wa matarsa Zeresh, da dukan abokansa, me ya same shi. Masu ba shi shawara, da matarsa Zeresh, suka ce masa, “Idan Mordekai, wanda ka fara fāɗuwa a gabansa, daga zuriyar Yahudawa yake, to, ba za ka yi nasara a kansa ba, tabbatacce za ka fāɗi a gabansa!”