Tsallake zuwa abun ciki

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da The Emblems of the Holy Spirit

14 ayoyi · 29 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

  1. Ya sāke cewa, “Mulkin Allah yana kama da haka. Wani mutum ya yafa iri a gona.

  2. A kwana a tashi har irin yă tsiro, yă yi girma, bai kuwa santa yadda aka yi ba.

  3. Ƙasar da kanta takan ba da ƙwaya, da farko takan fid da ƙara, sa’an nan ta fid da kai, sa’an nan kan yă fid da ƙwaya.

  4. Da suka ji wannan motsi, taro ya haɗu wuri ɗaya a ruɗe, domin kowannensu ya ji suna magana da yarensa.

  5. Cike da mamaki, suka yi tambaya suna cewa, “Ashe, duk waɗannan mutane masu magana ba Galiliyawa ba ne?

  6. To, yaya kowannenmu yana ji suna yarensa?

  7. Fartiyawa, Medes da Elamawa; mazaunan Mesofotamiya, Yahudiya da Kaffadokiya, Fontus da Asiya,

  8. Firjiya da Famfiliya, Masar da sassa Libiya kusa da Sairin; baƙi daga Roma

  9. (Yahudawa da kuma waɗanda suka tuba suka shiga Yahudanci); Kiretawa da Larabawa, mun ji su suna shelar abubuwan banmamaki na Allah da yarenmu!”

  10. Kamar dai yadda Ruhu Mai Tsarki ya ce, “Yau, in kuka ji muryarsa,

  11. kada ku taurare zukatanku, yadda kuka yi a tawayen nan, a lokacin gwaji a hamada,

  12. inda kakanninku suka gwada ni, suka kuma gwada ni, ko da yake a cikin shekaru arba’in sun ga abin da na yi.

  13. Shi ya sa na yi fushi da wancan zamani, na kuma ce, ‘Kullum zukatansu a karkace suke, ba su kuma san hanyoyina ba.’

  14. Saboda haka na yi rantsuwa a cikin fushina, ‘Ba za su taɓa shiga hutuna ba.’ ”