Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da The Emblems of the Holy Spirit: Cloven tongues
Ayoyi game da Cloven tongues
Da suka ji wannan motsi, taro ya haɗu wuri ɗaya a ruɗe, domin kowannensu ya ji suna magana da yarensa.
Cike da mamaki, suka yi tambaya suna cewa, “Ashe, duk waɗannan mutane masu magana ba Galiliyawa ba ne?
To, yaya kowannenmu yana ji suna yarensa?
Fartiyawa, Medes da Elamawa; mazaunan Mesofotamiya, Yahudiya da Kaffadokiya, Fontus da Asiya,
Firjiya da Famfiliya, Masar da sassa Libiya kusa da Sairin; baƙi daga Roma
(Yahudawa da kuma waɗanda suka tuba suka shiga Yahudanci); Kiretawa da Larabawa, mun ji su suna shelar abubuwan banmamaki na Allah da yarenmu!”