Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da The Apostles

43 ayoyi · 26 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Abin da na faɗa muku a asirce, ku faɗe shi a sarari; abin da aka faɗa muku a kunne, ku yi shelarsa daga kan rufin ɗaki.

  2. Kada ku ji tsoron masu kashe jiki amma ba sa iya kashe rai. A maimakon haka, ku ji tsoron Wannan wanda yake da iko yă hallaka rai duk da jiki a jahannama ta wuta.

  3. Ba akan sayar da kanari biyu kobo ɗaya ba? Duk da haka ba ɗayansu da zai fāɗi ƙasa ba da yardar Ubanku.

  4. Kai, ko gashin kanku ma duk an ƙidaya su.

  5. Saboda haka kada ku ji tsoro; kun fi kanari masu yawa, daraja nesa.

  6. “Duk wanda ya bayyana yarda a gare ni a gaban mutane, ni ma zan bayyana yarda a gare shi a gaban Ubana da yake cikin sama.

  7. Amma duk wanda ya yi mūsun sani na a gaban mutane, ni ma zan yi mūsun saninsa a gaban Ubana da yake cikin sama.

  8. “Duk wanda ya fi ƙaunar mahaifinsa ko mahaifiyarsa fiye da ni, bai dace yă zama nawa ba; duk kuwa wanda yake ƙaunar ɗansa ko diyarsa fiye da ni, bai dace yă zama nawa ba;

  9. duk wanda kuma bai ɗauki gicciyensa ya bi ni ba, bai dace yă zama nawa ba.

  10. Duk mai son adana ransa zai rasa shi, duk wanda kuwa ya rasa ransa saboda ni zai same shi.

  11. Suka iso Kafarnahum. Da yana cikin gida, sai ya tambaye su ya ce, “Gardamar me kuke yi a hanya?”

  12. Amma suka yi shiru, don a hanya suna gardama ne, a kan ko wane ne a cikinsu ya fi girma?

  13. Da Yesu ya zauna, sai ya kira Sha Biyun ya ce, “In wani yana so yă zama na fari, dole yă zama na ƙarshe duka, da kuma bawan kowa.”

  14. Ya ɗauki wani ƙaramin yaro ya sa yă tsaya a tsakiyarsu. Ya ɗauke shi a hannunsa, ya ce musu,

  15. “Duk wanda ya karɓi ɗaya daga cikin waɗannan ƙananan yara a cikin sunana, ni ya karɓa. Duk wanda kuma ya karɓe ni, ba ni ya karɓa ba, amma wanda ya aiko ni ne ya karɓa.”

  16. Gardama ta tashi a tsakaninsu, a kan ko wane ne a cikinsu ya fi girma.

  17. Yesu ya ce musu, “Sarakunan Al’ummai suna nuna iko a kan mutanensu, kuma waɗanda suke nuna iko a kansu, suna kiran kansu Masu Taimakon mutane.

  18. Amma ku, kada ku zama haka. A maimakon haka, sai dai wanda ya fi girma a cikinku, ya zama kamar wanda ya fi ƙanƙanta, wanda kuma ke mulki, ya zama kamar mai hidima.

  19. Wane ne ya fi girma? Wanda yake zaune a tebur ne, ko kuma shi da yake yin hidima? Ashe, ba wanda yake zaune a tebur ba ne? Amma ga ni, ni mai yin hidima ne a cikinku.

  20. Ku ne kuka tsaya tare da ni a gwaje-gwajen da na sha.

  21. Daidai kamar yadda Ubana ya ba ni mulki, haka ni ma nake ba ku.

  22. Saboda ku ci, ku sha a teburina a cikin mulkina. Kuma ku zauna a kan gadon sarauta, ku yi wa kabilu goma sha biyu na Isra’ila shari’a.

  23. Suka tashi nan da nan suka koma Urushalima. A can suka sami Sha Ɗayan nan da waɗanda suke tare da su a wuri ɗaya,

  24. suna cewa, “Gaskiya ne! Ubangiji ya tashi, ya kuma bayyana ga Siman”

  25. Sai su biyun nan suka ba da labarin abin da ya faru a hanya, da kuma yadda suka gane Yesu yayinda ya kakkarya burodin.