Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Shur

6 ayoyi · 1 fanni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

  1. Mala’ikan Ubangiji ya sami Hagar kusa da maɓulɓula a jeji, ita ce maɓulɓular da take gefen hanya zuwa Shur.

  2. Daga Mamre, Ibrahim ya kama hanya ya nufi wajajen Negeb, ya zauna a tsakanin Kadesh da Shur. Ya zauna a Gerar na ɗan lokaci,

  3. Zuriyarsa sun zauna tsakanin Hawila ne da Shur, wanda yake kusa da gabashin iyakar Masar wajen Asshur. Sun yi zaman rikici da dukan sauran ’yan’uwansu.

  4. Sai Musa ya jagoranci Isra’ila daga jan teku zuwa hamadar Shur. Kwana uku suka yi tafiya cikin hamada ba su sami ruwa ba.

  5. Sa’an nan Shawulu ya ci Amalekawa da yaƙi tun daga Hawila har zuwa Shur, a gabashin iyakar Masar.

  6. Dawuda da mutanensa suka haura suka yaƙi Geshurawa, da Girziyawa, da Amalekawa. (Waɗannan su ne mazaunan ƙasar a dā, tun daga Shur har zuwa ƙasar Masar.)