Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Self-Delusion

47 ayoyi · 23 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Idan kuma wani mutum ya ji kalmomi na wannan rantsuwa, ya kuma sa wa kansa albarka yana tunani cewa, “Ba abin da zai same ni, ko da na nace a taurinkaina.” Wannan zai jawo lalacewar dukan Isra’ila tare da kai.

  2. Sa’ad da aka tattara Isra’ilawa, aka kuma ba su guzuri, sai suka taka suka fita don su sadu da Arameyawa. Isra’ilawa suka kafa sansani ɗaura da su kamar ƙananan garkuna biyu na awaki, yayinda Arameyawa suka rufe dukan jejin.

  3. Ben-Hadad ya ce, “Zan mayar da biranen mahaifinka da na ƙwace daga mahaifinka. Za ka iya sa wurin kasuwarka a cikin Damaskus, kamar yadda mahaifinka ya yi a Samariya.” Ahab ya ce, “Bisa wannan yarjejjeniya zan sake ka.” Saboda haka ya yi yarjejjeniya da shi, sai ya bar shi ya tafi.

  4. Yakan ce wa kansa, “Ba abin da zai girgiza ni; kullum zan yi murna ba zan taɓa shiga wahala ba.”

  5. Yakan ce wa kansa, “Ai, Allah ya manta; ya rufe fuskarsa ba ya gani.”

  6. Sa’ad da nake lafiya, na ce, “Ba zan jijjigu ba.”

  7. Ko da yake yayinda yake a raye ya ɗauka kansa mai albarka ne, mutane kuma sun yabe ka sa’ad da kake cin nasara,

  8. “Amma mutanena ba su saurare ni ba; Isra’ila bai miƙa kansa gare ni ba.

  9. Saboda haka na ba da su ga zukatansu da suka taurare don su bi dabararsu.

  10. Akwai hanyar da ta yi kamar tana daidai ga mutum, amma a ƙarshe takan kai ga mutuwa.

  11. waɗanda sukan ɗauka su tsarkaka ne a ganinsu alhali kuwa ƙazamai ne su;

  12. Kika ce, ‘Zan ci gaba har abada, madawwamiyar sarauniya!’ Amma ba ki lura da waɗannan abubuwa ko ki yi la’akari a kan abin da zai faru ba.

  13. “To, yanzu fa, ki kasa kunne, ke mai ƙaunar nishaɗi, mai zama da rai kwance kina kuma ce wa kanki, ‘Ni ce, kuma babu wani in ban da ni. Ba zan taɓa zama gwauruwa ko in sha wahalar rashin ’ya’ya ba.’

  14. Duk waɗannan za su sha kanki cikin farat ɗaya, a rana guda, rashin ’ya’ya da gwauranci. Za su zo a kanki da cikakken minzani, duk da yawan masu dubanki da kuma dukan sihirinki.

  15. Kin dogara a muguntarki kika kuma ce, ‘Babu wanda ya gan ni.’ Hikimarki da saninki sun ɓad da ke sa’ad da kika ce wa kanki, ‘Ni ce, kuma babu wani in ban da ni.’

  16. Bala’i zai fāɗo a kanki, kuma ba za ki san yadda za ki rinjaye shi yă janye ba. Masifa za tă fāɗo a kanki da ba za ki iya tsai da ita da kuɗin fansa ba; lalacewar da ba ki taɓa mafarkinta ba za tă auko miki nan da nan.

  17. Kowanne yakan ce, “Zo, bari in samo ruwan inabi! Bari mu cika cikinmu da barasa! Gobe ma zai zama kamar yau, ko ma fiye da haka.”

  18. Sun yi ƙarya a kan Ubangiji; sun ce, “Ba zai yi kome ba! Ba wata masifar da za tă same mu; ba za mu taɓa ganin takobi ko yunwa ba.

  19. Lalle za mu aikata duk abin da muka ce za mu yi. Za mu ƙone turare ga Sarauniyar Sama za mu kuma miƙa hadayun sha gare ta kamar dai yadda mu da kakanninmu, sarakunanmu da fadawanmu muka yi a garuruwan Yahuda da kuma kan titunan Urushalima. A lokacin muna da abinci a yalwace muna kuma da arziki ba mu kuma da wata damuwa.

  20. Efraim ya haɗa kai da gumaka; ku ƙyale shi kurum!

  21. Efraim yana fariya yana cewa, “Ni mai arziki ne ƙwarai; na azurta. Da dukan wadatata ba za a sami wani laifi ko zunubi a gare ni ba.”

  22. Kada ma ku yi tunani a ranku cewa, ‘Ai, Ibrahim ne mahaifinmu.’ Ina gaya muku cewa Allah zai iya tā da ’ya’ya wa Ibrahim daga cikin duwatsun nan.

  23. “Ba duk mai ce mini, ‘Ubangiji, Ubangiji,’ ne zai shiga mulkin sama ba, sai dai wanda yake aikata nufin Ubana da yake sama.

  24. Da yawa za su ce mini a wannan rana, ‘Ubangiji, Ubangiji, ashe, ba mu yi annabci a cikin sunanka ba, ba kuma a cikin sunanka ne muka fitar da aljanu, muka yi abubuwan banmamaki da yawa ba?’

  25. Sa’an nan zan ce musu a fili, ‘Ban taɓa saninku ba. Ku rabu da ni, ku masu aikata mugunta!’