Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Seed: Every herb, tree and grass yields its own
Ayoyi game da Every herb, tree and grass yields its own
Sa’an nan Allah ya ce, “Bari ƙasa tă fid da tsire-tsire, da shuke-shuke, da itatuwa a bisa ƙasa masu ba da amfani da ’ya’ya a cikinsu, bisa ga irinsu.” Haka kuwa ya kasance.
Ƙasar ta fid da tsire-tsire, da shuke-shuke masu ba da ’ya’ya bisa ga irinsu, ta fid kuma da itatuwa masu ba da ’ya’ya da iri a cikinsu bisa ga irinsu. Allah ya ga yana da kyau.
Sa’an nan Allah ya ce, “Ga shi, na ba ku kowane tsiro mai ba da ’ya’ya masu kwaya da suke a fāɗin duniya, da dukan itatuwa masu ba da ’ya’ya, don su zama abinci a gare ku.