Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Raisin

4 ayoyi · 4 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

  1. Abigiyel ba tă ɓata lokaci ba. Ta ɗauki burodi guda ɗari biyu, da salkar ruwan inabi biyu da tumaki biyar da aka gyara, da soyayyen hatsi mudu biyar, da waina guda ɗari na ’ya’yan inabi, da masa ɗari biyu na kauɗar ɓaure ta labta wa jakuna.

  2. Suka ba shi saura wainan ’ya’yan ɓaure da kuma wainan ’ya’yan inabi, ya ci ya sami ƙarfi. Gama bai ci ba, bai sha ba, har yini uku da dare uku.

  3. Sa’ad da Dawuda ya yi ɗan nesa da ƙwanƙolin, sai ga Ziba mai hidimar Mefiboshet, yana jira yă tarye shi. Yana da jerin jakuna da sirdi suna ɗauke da dunƙulen burodi ɗari biyu, da ƙosai busasshen inabi ɗari ɗaya, da kosan ’ya’yan itace ɓaure guda ɗari, da salka ruwan inabi.

  4. Haka ma, maƙwabtansu daga nesa har Issakar, Zebulun da Naftali suka zo suka kawo abinci a kan jakuna, raƙuma, alfadarai da shanu. Akwai tanadin mai yawa na gari, kauɗar ɓaure, nonnan busassun ’ya’yan inabi, ruwan inabi, mai, shanu da tumaki. Duk an yi haka don a nuna farin ciki ƙwarai a cikin dukan ƙasar Isra’ila.