Skip to content

Ayoyin Littafi Mai Tsarki game da Publicans

32 ayoyi · 19 fannoni

Mahimman ayoyin Littafi Mai Tsarki

Tace bisa littafi
  1. Saboda haka, ya yi gaba da gudu, kuma ya hau itacen sikamo, don yă gan shi, tun da Yesu zai bi wannan hanyar ne.

  2. Da Yesu ya iso wurin, sai ya ɗaga ido sama, ya ce masa, “Zakka, ka yi maza ka sauka. Ni kam, dole in sauka a gidanka yau.”

  3. Sai ya sauka nan da nan, ya karɓe shi da murna.

  4. Dukan mutane suka ga haka, kuma suka fara gunaguni, suka ce, “Ya je don yă zama baƙon ‘mai zunubi.’ ”

  5. Amma Zakka ya tashi a tsaye, ya ce wa Ubangiji, “Duba, Ubangiji! Nan take, rabin dukiyar da nake da shi, na ba wa matalauta. In kuma na taɓa cutan wani, a kan wani abu, zan mayar da shi ninki huɗu.”

  6. Sai Yesu ya ce masa, “Yau, ceto ya zo gidan nan, domin wannan mutum shi ma ɗan Ibrahim ne.

  7. Saboda Ɗan Mutum ya zo ne, domin yă nemi abin da ya ɓata, yă cece shi kuma.”